A rana daya ‘Yan bindiga su ka kashe fiye da adadin da COVID-19 ta kashe - Hon. Kazaure

A rana daya ‘Yan bindiga su ka kashe fiye da adadin da COVID-19 ta kashe - Hon. Kazaure

- Muhammad Gudaji Kazaure ya soki yadda ake yakin COVID-19 a Najeriya

- ‘Dan siyasar ya ce ya kamata gwamnati ta fi maida hankali wajen tsare rai

- Gudaji Kazaure ya kuma yi tir da yadda aka rufe garuruwa saboda annobar

Muhammad Gudaji Kazaure mai wakiltar mazabun Kazaure, Roni, Gwiwa da ‘Yankwashi a jihar Jigawa ya tofa albarkacin bakinsa game da yaki da ake yi da annobar COVID-19.

Honarabul Muhammad Gudaji Kazaure ya yi Allah-wadai da yadda gwamnati ta damu da cutar Coronavirus fiye da yadda ake kokarin magance matsalar rashin tsaro a fadin kasar.

Gudaji Kazaure ya na sanye da takunkumin rufe fuska, ya mike ya na cewa: “Bakin mutum ya na da karfin lafiya, ban yarda da wata Coronavirus ba, babu cutar da za ta taba ni.”

“Abin da na yarda shi ne, dubi yadda mu ka damu da COVID-19, me zai hana gwamnatin nan ta damu da kashe-kashen jama’a kamar yadda ta damu da annobar cutar COVID-19?”

KU KARANTA: Yadda Coronavirus ta harbi wani yaro ‘Dan shekara 3 da haihuwa

Shararren ‘dan majalisar wakilan kasar ya ke cewa: “Ku na batun COVID-19, Ana maganar miyagun da a rana guda rak su ka yi kisan da ta zarce ta annobar COVID-19 a Najeriya.”

“Mutane sun damu da wannan COVID-19; a rufe fuskoki, a zauna a gida, a garkame gari. Babu dalilin rufe garuruwanmu. Kamata ya yi a rufe ko ina dalilin kashe-kashen da ake yi.”

‘Dan siyasar ya na ganin idan har za a rufe gari, ya kamata ne ayi wannan domin kawo karshen rashin tsaro. A cewarsa wannan matsala ta na warware nasarar da gwamnati ta samu.

“Abin da gwamnati ta ke yi na raba kaya domin rage radadi da kuma yin ayyukan more rayuwa domin kawo canji zai tashi a tutar babu a sakamakon barnar da ‘yan bindiga su ke yi.”

Mun fahimci cewa Muhammad Gudaji Kazaure ya yi wannan magana ne a ranar Alhamis 4 ga watan Yuni, 2020, a lokacin da 'yan majalisa su ka tattauna game da harkar rashin tsaro.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel