Ganduje ya kaddamar da shirin 'Ruga' a jihar Kano (Hotuna)

Ganduje ya kaddamar da shirin 'Ruga' a jihar Kano (Hotuna)

Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya kaddamar da shirin fara gina katafariyar 'Ruga' domin amfanin makiyaya a jihar Kano.

Katafariyar 'Rugar', wacce aka fara ginawa a dajin Yansoshi da ke karamar hukumar Kiru, za ta kunshi gidaje 200, makarantu, asibiti, ofishin 'yan sanda, babban dam domin shayar da dabbobi da sauransu.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Salihu Tanko Yakasai, mai taimakawa gwamna Ganduje a bangaren yada labarai, ya wallafa a shafinsa na Tuwita.

A cikin sanarwar, Yakasai ya ce ana gina wata 'Rugar' a dajin Falogore da ke karkashin karamar hukumar Doguwa.

Gwamnatin tarayya ce ta fara zuwa da shirin samar da 'Ruga' a jihohi domin kawo karshen yawaitar samun rikici a tsakanin makiyaya da manoma.

Sai dai, shirin ya sha suka a wurin wasu 'yan Najeriya, musamman shugabanni da jagororin al'umma daga kudancin Najeriya.

Gwamnonin jihohin kudancin Najeriya da dama sun fito fili sun nuna adawarsu ga shirin gwamnatin tarayya na amfani da filayen jihohinsu domin ginawa makiyaya 'Ruga'.

Ma su adawa da shirin 'Ruga' na kafa hujja ne da cewa ana kokarin daukaka wata kabila ta hanyar mallaka musu filaye da wurin zama a jihohin da ba nasu ba.

Ganin haka ne yasa gwamnatin tarayya ta bar shirin samar da 'Ruga' a hannun gwamnonin jihohi.

DUBA WANNAN: An kama matashi mai shekaru 25 ya na yi wa dattijuwa mai shekaru 85 fyade a karamar hukumar Rafi

Ya zuwa yanzu, wasu jihohin arewa sun fara shirye - shiryen fara samar da 'Ruga' domin amfanin makiyaya.

'Ruga' za ta kunshi abubuwa da wurare da makiyaya ke nema ko bukata domin gudanar rayuwa da harkokinsu na kiwo.

Makiyaya za su ke biyan gwamnatin kudin haraji domin samun damar shiga 'Ruga' domin kiwon dabbobinsu ba tare da sun shiga gonakin manoma ba, lamarin da ya dade yana haddasa rikicin manoma da makiyaya.

Ganduje ya kaddamar da shirin 'Ruga' a jihar Kano (Hotuna)
Ganduje yayin kaddamar da shirin fara ginin 'Ruga' a jihar Kano
Asali: Twitter

Ganduje ya kaddamar da shirin 'Ruga' a jihar Kano (Hotuna)
Ganduje ya kaddamar da shirin 'Ruga' a jihar Kano
Asali: Twitter

Ganduje ya kaddamar da shirin 'Ruga' a jihar Kano (Hotuna)
Ganduje a 'Ruga' ta jihar Kano
Asali: Twitter

Ganduje ya kaddamar da shirin 'Ruga' a jihar Kano (Hotuna)
Ganduje ya na gwadawa mataimakinsa sharo yayin kaddamar da ginin katafariyar 'Ruga' a dajin Falgore.
Asali: Twitter

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel