Jerin jihohin Arewa 3 da suka sallami dukkan masu Koronansu

Jerin jihohin Arewa 3 da suka sallami dukkan masu Koronansu

Kimanin watanni uku yanzu da cutar nan mai toshe numfashi da ta addabi duniya watau Coronavorus ko COVID-19 ta bulla a Najeriya.

Alkaluma sun fara nuna an fara samun nasara kan yaki da cutar musamman a Arewacin Najeriya duk da cewa yankin ce kusa ta karce da ta samu bullar cutar a Najeriya.

Kawo yanzu, Najeriya ta samu mutane 11,844 da suka kamu da cutar Coronavirus. Yayinda 3,696 sun samu sauki kuma an sallamesu, 333 sun rigamu gidan gaskiya, a cewar alkaluman hukumar hana yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC.

Legit.ng Hausa tana mai kawo muku jerin jihohin Arewa uku da suka alanta sallamar dukkan masu fama da cutar a jihar kuma babu sauran mai cutar a jihohin.

KU KARANTA: Mun sallami karin masu cutar Korona 30 a Abuja - Ministan FCT

1. Jihar Kebbi

A ranar Alhamis, 28 ga Mayu, Kwamitin kar ta kwanan yakar cutar COVID-19 na jihar Kebbi, a ranar Alhamis ya sallami mutum biyu na karshe masu dauke da cutar ta Coronavirus a jihar.

Shugaban kwamitin wanda shine kwamishanan lafiyan jihar, Jafar Muhammad, ya bayyana hakan ne a cibiyar killace masu cutar dake Asibitin KMC dake Kalgo, jihar Kebbi.

Yace: "Mutane biyu masu cutar Coronavirus da suka rage a cibiyar killacewarmu dake asibitin KBC Kalgo sun samu sallama yau, Alhamis, 28/5/2020."

2. Jihar Zamfara

Jihar Zamfara ta sallama majinyata biyar da suka rage mata masu fama da cutar korona a ranar 29 ga watan Mayun 2020.

Kamar yadda hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa ta Najeriya (NCDC) ta bayyana, jihar ta fara samun mutane biyu dauke da cutar ne a ranar 24 ga watan Afirilun 2020.

A lokacin kuwa Najeriya na da mutum 1,095 a fadin jihohi 27 wadanda ke dauke da muguwar cutar.

Jimillar adadin wadanda suka kamu da cutar a Zamfara 76. Yayinda 71 suka samu waraka kuma aka sallamesu, 5 sun mutu.

SHIN KA SANYadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi, latsa nan

3. Jihar Sokoto

A ranar Alhamis ne gwamnatin jihar Sokoto ta fitar da sanarwar cewa dukkan ma su dauke da kwayar cutar korona a jihar sun warke sarai.

Hakan na kunshe ne a cikin wani takaitaccen sako da ma'aikatar lafiya ta jihar Sokoto ta wallafa a shafinta da ke manhajar Tuwita.

A cikin sanarwar, gwamnatin jihar ta sanar da cewa an sallami sauran mutane biyar da ke zaman jinyar cutar korona a cibiyar killacewa domin su koma gidajensu, wurin iyalansu.

Mutane 101 ne aka tabbatar da cewa sun kamu da kwayar cutar korona a jihar Sokoto tun bayan bullar cutar, mutane 14 ne cutar ta yi sanadiyar mutuwarsu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel