An samu mai shekara 3 da ya kamu da ciwon COVID-19 a Jihar Imo - Kwamiti

An samu mai shekara 3 da ya kamu da ciwon COVID-19 a Jihar Imo - Kwamiti

A jihar Imo, an samu wani yaro da bai wuce shekara uku da haihuwa ba da ya kamu da cutar COVID-19. Kawo yanzu wannan cuta ta addabi kasashen Duniya da-dama.

Shugaban kwamitin yaki da annobar cutar Coronovirus a jihar Imo, Farfesa Maurice Iwu, ya tabbatar da wannan labari maras dadi na karamin yaro da cutar ta harba.

Maurice Iwu ya shaidawa manema labarai wannan ne a tsakiyar makon da ya gabata. Shugaban kwamitin yaki da cutar ya yi wannan jawabi ne a babban birnin jihar Imo.

Iwu wanda ya taba rike hukumar zabe na kasa watau INEC, ya ce bayan yaron da aka samu dauke da COVID-19, gwaji ya nuna mahaifinsa da kuma ‘yanuwansa sun kamu.

Farfesan ya ce ‘yanuwan wannan yaro har su uku ne cutar ta kama, sannan kuma da mahaifinsu. Ya ce gwamnati ta na bada kula na musamman ga wannan karamin yaro.

KU KARANTA: COVID-19: El-Rufai ya fara duba yiwuwar bude Jihar Kaduna

A halin yanzu akwai mutane bakwai da su ke jinya a babban asibitin tarayya da ke garin Owerri kamar yadda shugaban wannan kwamiti ya shaidawa ‘yan jarida a zantawar.

“Ya na da muhimmanci a jaddada cewa Coronavirus gaskiya ce, amma ba hukuncin kisa ba ce.”

Farfesa Iwu ya kuma kara da cewa: “Kwamitinmu ya fara samun kira daga jama’a, ana bayyana mana wadanda ba su da lafiya.” Ya ce su kan bibiyi gaskiyar wadannan magana.

“Kwamitin ya zo ne domin ya yi aiki. Mu na kokarin dakile yaduwar cutar Coronavirus.”

“Mu na kira ga mutane su cigaba da bin matakan kariya daga annobar kamar yawan wanke hannu da ruwan fanfo, amfani da man wanke hannu tare da kauracewa cinkoso.”

A karshe shugaban wannan kwamiti ya yi kira ga mutanen Imo su rika rufe fuskokinsu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel