Shugaban PSC, Musiliu Smith ya yi babban rashi

Shugaban PSC, Musiliu Smith ya yi babban rashi

Uwargidan shugaban Hukumar Kula da Al'amuran 'Yan sandan Najeriya, PSC, Alhaji Musiliu Smith ta rasu.

Alhaja Ariat Aderoju Smith ta rasu ne a ranar Juma'a 6 ga watan Yunin shekarar 2020 kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Ta rasu tana da shekaru 69 a duniya.

Sanarwar da babban sakataren watsa labarai na gwamnan Legas, Gboyega Akosile, ya fitar ta ce za ayi jana'izar Alhaja Smith a yau Asabar bisa koyarwar addinin musulunci.

Shugaban PSC, Musiliu Smith ya yi babban rashi
Shugaban PSC, Musiliu Smith ya yi babban rashi. Hoto daga The Nation
Asali: UGC

KU KARANTA: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

A cewar sanarwar, iyalanta ne kawai za a bari su hallarci jana'izar saboda biyaya da dokar da hukumar NCDC da gwamnatin Legas suka bayar na bayar da tazara don dakile yaduwar COVID-19.

"Gwamnatin jihar Legas, a madadin iyalan Smith na sanar da rasuwar mahaifiyarmu kuma kaka, Alhaja Ariat Aderoju Smith (nee Jinadu) wacce ta rasu a ranar Juma'a tana da shekaru 69.

"Marigayiyar ta rasu ta bar mijinta, Alhaji Musliu A.K. Smith, tsohon Sufeta Janar na Yan sanda kuma shugaban PSC.

"Sai yayanta Mr Mujeed Adekunle Smith da Mrs Atiat Olubunmi Sheidu. Allah ya jikanta da rahama ya saka mata da Jannatul Firdausi," in ji sanarwar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel