Buhari ya yi muhimmin nadi a ma'aikatar Pantami

Buhari ya yi muhimmin nadi a ma'aikatar Pantami

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Farfesa Umar Garba Danbatta don shugabantar NCC

- Ministan sadarwa da tattalin arziki mai dogaro da fasahar zamani, Dr Isa Ali Ibrahim Pantami ne ya mika bukatar

- Kamar yadda ma'aikatar ta wallafa a shafinta na twitter, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin a ranar 5 ga Yunin 2020

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Farfesa Umar Garba Danbatta a matsayin mataimakin shugaban hukumar sadarwa ta Najeriya (NCC).

Ministan sadarwa da tattalin arziki mai dogaro da fasahar zamani, Dr Isa Ali Ibrahim Pantami ne ya mika bukatar kamar yadda dokar hukumar sadarwa ta Najeriya ta 2003 ta gindaya.

Kamar yadda shafin ma'aikatar sadarwa da tattalin arziki mai dogaro da fasahar zamani na Twitter ya bayyana, Pantami ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin a ranar Juma'a, 5 ga watan Yunin 2020.

Pantami ya bayyana cewa, an yi wannan nadin ne don cimma manufa da tsare-tsaren tattalin arziki mai dogaro da fasahar zamani.

Ministan ya yi kira ga wanda aka nada din, "ya karfafa tare da inganta ma'aikatar NCC tare da tabbatar da tsare-tsaren gwamnatin tarayya ta hanyar ma'aikatar."

KU KARANTA: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

A wani labari na daban, fitaccen marubuci dan Najeriya, Farfesa Wole Soyinka ya ce bai yarda Shugaba Muhammadu Buhari ne ke juya akalar mulki a kasar ba.

Da ake hira ta da shi a ranar Alhamis a PlusTv Africa, marubucin ya ce abinda zai magance matsalolin Najeriya shine rage karfin da gwamnatin tarayya ke da shi tare da karfafa.

Ya kuma kara da cewa akwai bukatar mutane su fahimci tarihin inda kasa ta fito da inda aka dosa, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Soyinka yana martani ne a kan budediyar wasikar da Umar Dangiwa, tsohon gwamnan soji na jihar Kaduna ya aikewa Buhari inda ya yi magana kan yadda shugaban kasar ke son nada mutanen da suka fito daga yankinsa mukami.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel