Bayan makonni 10, Buhari ya halarci Sallar Juma'a a fadar shugaban kasa (Hotuna)

Bayan makonni 10, Buhari ya halarci Sallar Juma'a a fadar shugaban kasa (Hotuna)

Bayan kimanin makonni goma bayan rufe dukkan Masallatai da majam'iu a birnin tarayya Abuja, shugaba Muhammadu Buhari ya halarci Sallar Juma'a a yau 5 ga watan yuni, 2020.

Hotuna daga hadiminsa kan sabbin kafafen yada labara, Bashir Ahmad, sun nuna yadda shugaban kasan ya Sallaci farillar Juma'a tare da mukarrabansa.

An gudanar da Sallan ne cikin Masallacin fadar shugaban kasa dake Aso Villa, birnin tarayya Abuja.

Kalli hotunan:

Bayan makonni 10, Buhari ya halarci Sallar Juma'a a fadar shugaban kasa (Hotuna)
Hoto daga Bashir Ahmad
Asali: Twitter

TSOKACI: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

KU KARANTA: Babu wanda ya sauya sheka zuwa PDP daga APC - Kakakin APC ta yi martani

A ranar 1 ga watan yuni, 2020, Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da shawarar kwamitin kar ta kwanan fadar shugaban kasa kan cutar COVID-19 PTF na sassauta dokokin da aka kafa domin takaita yaduwar cutar.

Shugaban kwamitin wanda shine sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, ya sanar da cewa an sun gana da shugaba Buhari kuma sun bashi shawara kan matakin da za'a dauka gaba.

Bayan ganawar, Shugaban kasa ya amince da bude wuraren Ibada (Masallatai da Majami'u kadai) da kasuwanni a fadin tarayya amma da sharadin za a bi dokokin da hukumar NCDC ta gindaya.

Yace: "PTF ta mika shawarinta kuma shugaba Muhammadu Buhari ya rattafa hannu a aiwatar da su cikin makonni hudu masu zuwa fari daga ranar 2 zuwa 29 ga watan Yuni, 2020."

"An sassauta dokar hana taruwa a wuraren Ibada bisa ga sharudan da PTF ta gindaya da kuma yardar gwamnatocin jihohi."

"Za'a amince a rika shiga kasuwanni da wuraren tattalin arziki amma da lura saboda takaita yaduwar."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel