Babu wanda ya sauya sheka zuwa PDP daga APC - Kakakin APC ta yi martani
Jam‘iyyar All progressives Congress APC ta jihar Kwara ta karyata rahotannin da KE yaduwa a kafafen yada labarai cewa ’yayan jamiyyar 10,000 sun sauya sheka zuwa jam’iyyar adawa ta People’s Democratic Party PDP.
Kakakin jam’iyyar na jihar, Alhaji Tajudeen Aro ya bayyana hakan ne a jawabin da ya saki ranar Juma’a a garin Ilori cewa “labarun karya dake yaduwa cewa mutane 10,000 sun sauya sheka daga APC zuwa PDP ba komai bane illa Almara.”
“Wannan ikirarin da PDP keyi abin dariya ne saboda ta yaya mutane 10,000 za su tara kansu cikin wannan hali da ake ciki na annobar Korona ba tare da sanin al’umma ba.”
”PDP za ta iya cigaba da mafarkinta har tsawon shekaru 7 masu zuwa.”
”Muna kira ga jama’a suyi watsi da rahotannin karyan jamiyyar adawa dake kokarin amfani da dan karamin rashin jituwan da ke faruwa cikin APC wajen bata mata suna.”
A ranar Alhamis mun kawo muku labarin cewa Dubban 'yan jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Kwara a ranar Alhamis sun sauya sheka sun koma jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP).
Wadanda suka sauya shekan sun fito ne daga mazabar Kwara ta Arewa kamar yadda The Nation ta ruwaito.
Tsaffin yan jamiyyar na APC a baya bayan nan sun nuna rashin jin dadinsu da yadda rikici ya yi yawa a jamiyyar tun bayan da Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya karbi mulki.
Wadanda suka hallarci taron wakilai ne da aka zabo daga kananan hukumomi biyar da ke karkashin mazabar ta Kwara ta Arewa don biyaya ga sharrudan dakile yaduwar korona a cewar shugabansu Hon. Manzuma Kawu Dogo.
Abinda ya bayyana karara cikin lamarin nan shine akwai rikici tsakanin yan cikin gidan APC a jihar Kwara kuma na son ballewa.
Idan Baku manta ba, APC ta lashe zaben jihar Kwara ne a shekarar 2019 bayan kayar PDP dake karkashin jagorancin tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng