An damke wani mutum yana kokarin luwadi da mara lafiya (Bidiyo)

An damke wani mutum yana kokarin luwadi da mara lafiya (Bidiyo)

Dubun wani mutum ya cika a jihar Edo yayinda aka damkeshi yana kokarin zakkewa wani Mara lafiya dake wurinsa a unguwar Ikpoba dake babbar birnin jihar.

Mutumin wanda ya bayyana sunansa matsayin Alhaji ya yi kokarin luwadi da dan matashin ne da sunan fanshe alherin da yayi masa na siyan masa Tirela.

A cewar jaridar Vanguard, mara lafiyan ya laburta cewa Alhajin yayi masa alkawarin fiya da shi kasar waje ne da kuma shigar da shi harkar da yakeyi na safarar kwayoyi, kuma ya amince.

Yace Alhajin ya yi masa bayanin cewa cikin duburarsa za a sanya kwayoyin. Da ya tambayesa ta yaya hakan zai yiwu, sai ya ce kada ya damu zai nuna masa.

Ana nan sai matashin ya fadi rashin lafiya sai Alhajin ya kirashi cewa ga yi nan hanyar zuwa gidanshi.

Da ya isa gidan, sai ya fadawa matashin cewa ya zo ne domin koya masa yadda ake boye kwayoyin cikin dubura.

Abin mamaki, sai Alhajin ya fara shafa masa jiki kuma yace ya cire wandonsa. Kawai sai yayi kokarin tura azzakarinsa cikin duburan amma taki shiga kafin aka damkeshi.

Kalli bidiyon:

TSOKACI: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng

Tags: