'Yan bindiga sun kashe mutane 21, sun jikkata 12 a wani sabon hari da ya auku a kauyukan Zamfara

'Yan bindiga sun kashe mutane 21, sun jikkata 12 a wani sabon hari da ya auku a kauyukan Zamfara

Ana zargin wasu gungun 'yan daban daji sun yi wa wasu kauyuka a jihar Zamfara shigar ba zata, inda suka sheke ayarsu wajen zartar da mummunan ta'addanci a kan al'umma.

Mun samu cewa wasu 'yan bindiga sun hallaka mutum 21 tare da jikkata wasu mutane 12, a yayin wani mummunan hari da suka kai wasu kauyuka na jihar Zamfara.

'Yan bindiga sun dugunzuma hankalin al'umma a kauyukan da ke karkashin kananan hukumomin Maru da Talata Mafara a jihar Zamfara kamar yadda Channels TV ta ruwaito.

KARANTA KUMA: Ofishin kasafi: N9b aka ware domin gyara ginin Majalisar Tarayya ba N27b ba

Yayin ganawa da manema labarai, kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Muhammadu Shehu, ya ce hare-haren sun auku ne da manufar satar shanu a tsakanin ranar 2 da 3 na watan Yuni.

Shehu ya ce kauyukan da 'yan bindigar suka kai hari a karamar hukumar Maru sun hadar da Tungar Malan, Manyan Karaje, Tungar Arne, Dangodon Maiyakane, Dangodon Mai Masallaci da kuma Boleke.

Sansanin 'Yan daban daji
Hakkin Mallakar Hoto: Channels TV
Sansanin 'Yan daban daji Hakkin Mallakar Hoto: Channels TV
Asali: Twitter

Yana mai cewa, rayuka sun salwanta ne sakamakon fito-na-fito na dakarun 'Yan sa-kai suka yi da maharan, inda aka rika ruwan harsashi na bindiga babu kakkautawa.

Ya ci gaba da cewa, wannan fito-na-fito ta janyo salwantar rayukan mutane 15 yayin da wasu mutum bakwai suka jikkata, wanda a halin yanzu su na ci gaba da samun kulawa a asibiti.

Haka kuma kakakin rundunar 'yan sandan ya bayyana cewa, harin da 'yan bindiga suka kai kauyukan karamar hukumar Talata Mafara, ya salwantar da rayukan mutum 6 yayin da 5 suka jikkata.

DUBA WANNAN: Yadda za ka rika samun labaran Legit.ng Hausa a shafinka ana wallafawa

Kauyukan da aka kai harin a karamar hukumar Talata Mafara sun hadar da Gidan Dan Kani, Tungar lauti, Inwala da kuma Dangodo.

Babban jami'in 'yan sandan ya yi bayanin cewa, 'yan bindiga sun kai munanan hare-haren ne a yayin da al'umma ke dawo wa daga wata sallar Jana'iza.

A halin yanzu bincike ya yi nisa domin bankado miyagun da suka zartar da harin a baya-bayan nan, kuma za su fuskanci hukunci daidai da abinda suka aikata inji Kakakin na 'yan sanda.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel