COVID-19: Za a fara gwajin gida-gida a Kano

COVID-19: Za a fara gwajin gida-gida a Kano

Gwamnatin jihar Kano, karkashin jagorancin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta ce za ta fara bi gida-gida don yi wa jama'ar jihar gwajin coronavirus.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya sanar da hakan yayin zantawa da manema labarai don bada bayanai a kan inda aka kwana a kan cutar korona a jihar.

Abdullahi Umar Ganduje ya ce, gwajin gida-gidan zai taka rawar gani wajen kawo karshen annobar a jihar Kano.

Da yake wasu kananan hukumomi uku na jihar nan aka fi samun masu cutar a jihar, ya ce daukan matakin gwajin gida-gida ne kadai mafitar dakile yaduwar muguwar cutar.

Kananan hukumomin Nasarawa, Tarauni da Municipal ne aka fi samun masu cutar, cewar Ganduje.

Kwamishinan yada labarai na jihar Kano, Malam Muhammad Garba, ya sanar da BBC cewa adadin masu kai kansu asibiti don yin gwajin cutar da kansu ya yi kasa. Hakan ne yasa gwamnati za ta fara gwajin gida-gida.

Garba ya ce, "Za mu fara bibiyar mutane har gida don gwajin. Za mu fara da karamar hukumar Nasarawa saboda masu cutar sun fi yawa a nan."

COVID-19: Za a fara gwajin gida-gida a Kano
COVID-19: Za a fara gwajin gida-gida a Kano. Hoto daga BBC
Asali: Facebook

KU KARANTA: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

"Kafin mu fara gwajin, za a fara ba wa ma'aikatan kiwon lafiya babban horo don sanin yadda za a gudanar da gwajin."

Malam Mohammed Garba ya kara da cewa, "Matukar aka fara gwajin gida-gidan a kananan hukumomi uku da cutar ta fi kamari, su ma sauran kananan hukumomin jihar za a zagaya don yin gwajin."

Gwamnatin jihar Kano ta dauka wannan matakin ne bayan kwanaki kadan da bada umarnin bude kasuwanni da wuraren bauta a ranakun Laraba, Juma'a da Lahadi bayan shafe dogon lokaci a rufe.

A wani labari na daban, Shugaban kwamitin yaki da annobar korona ta jihar Kano, Dr Tijjani Hussein, ya bayyana cewa makonni kadan suka rage cutar ta yi kaura daga jihar Kano.

Hussein, wanda ya bayyana hakan a yayin tattaunawa a kan inda aka kwana a kan cutar a jihar Kano a ranar Alhamis, ya yi kira ga mazauna jihar da su dauka matakan dakile yaduwar cutar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel