Yadda na yi wa Jonathan waka amma na fada tsananin rudani - Nazifi Asnanic

Yadda na yi wa Jonathan waka amma na fada tsananin rudani - Nazifi Asnanic

Fitaccen mawakin Hausa Nazifi Asnanic ya bayyana wa BBC cewa cikin tarihin wakokin da ya rera, ba zai taba mantawa da wakar da ya yi wa Goodluck Jonathan, tsohon shugaban kasar Najeriya ba.

Duk da dai mawakin ya ce ya fi kaunar wakar da ya yi wa Dr Rabiu Musa Kwankwaso, amma ya ce wacce ya yi wa Jonathan ta matukar tsaya masa a rai sakamakon halin da ya fada bayan nan.

Fitaccen mawakin ya sanar da hakan ne a hirar da yayi da BBC kai tsaye a shafinsu na Instagram.

Kamar yadda yace, ya rera wa Jonathan waka ta yi karfi amma sai shekarar 2015 ta iso kuma "Masu son Buhari sun taru sun yi min yawa."

Asnanic ya ce a lokacin ya shiga rudani saboda wakar Jonathan ta ƙi bacewa, "ga shi kuma muna son mu yi tallan Buhari. Wannan ya sa ba zan iya mantawa da wakar ba," in ji shi.

Nazifi ya ce bai taba da-na-sanin yin wakar ba saboda zamanin mulkin Jonathan ne ya rera ta. Ya kuma kaunaci yadda ya rubuta ta.

Hakazalika, shahararren mawakin ya tabbatar da cewa wakar da ya rera wa Kwankwaso ba za ta taba bace masa ba.

Ya kara da cewa, yana matukar jin dadinta kuma yana alfahari da ita. "Kowacce kasa na ziyarta, kafin a fada min wata waka, ita ake fara wa da ita."

Yadda na yi wa Jonathan waka amma na fada tsananin rudani - Nazifi Asnanic
Yadda na yi wa Jonathan waka amma na fada tsananin rudani - Nazifi Asnanic. Hoto daga BBC
Asali: Instagram

KU KARANTA: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

An haifi mawaki Asnanic kimanin shekaru 33 da suka gabata a Durumin Iya da ke jihar Kano. A nan ya fara karatun allo da na boko.

Cikakken sunansa kuwa Nazifi Abdussalam Yusuf amma ya samo Asnanic ne ta hanyar dauko wasu bakake daga sunayen mutane uku.

Fitaccen mawakin ya ce ya fara waka ne don son da yake ya bayar da gudumawa ga al'umma. Amma kafin nan, ya kwashe lokaci mai tsayi yana rubuta waka kafin ya fara rerawa.

Mawakin ya ce tsoron kyamara ce ta sa baya fitowa a fina-finai.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel