Ba ni da burin da ya wuce in zama mashahuriyar 'yar kasuwa - Jaruma Rayya

Ba ni da burin da ya wuce in zama mashahuriyar 'yar kasuwa - Jaruma Rayya

Jaruma Surayya Aminu, wacce ake kira da Rayya a cikin shiri mai dogon Zango mai suna Kwana Casa'in na tashar Arewa24, ta ce tana fatan zama fitacciyar 'yar kasuwa.

Jarumar ta bayyana hakan ne yayin da tayi hira da BBC a shafinsu na Instagram.

Duk da 'yar wasan Hausan ta ce a jihar Legas aka haifeta kimanin shekaru 21 da suka shude, ta ce a jihar Kaduna ta girma.

Surayya ta ce shahararta ya bayyana ne sakamakon fitowa da ta yi a shiri mai dogon zango na Kwana Casa'in, amma ta fara harkar fim tun watanni shida kafin nan.

"Na yi fina-finai irinsu Hanyar Arziki, Yarena, Kanin Miji da sauransu," in ji ta.

Duk da haka, ta ce tun tana karama ta ke fatan zama 'yar jarida, wanda hakan ne yasa ta fara sha'awar shiga harkar fim.

Kamar yadda Surayya ta ce, jaruminta shine Ali Nuhu a maza amma a mata Rahama Sadau da Fati Muhammad ne madubin dubawarta.

Ta ce tana karatun difloma a bangaren jarida amma tana da burin ci gaba har zuwa matakin digiri ko fiye da haka.

Duk da tana kasuwanci a fannin samar da wutar lantarki daga kimiyyar rana, ta ce tana da burin zama hamshakiyar 'yar kasuwa kuma fitacciyar 'yar jarida.

Ba ni da burin da ya wuce in zama mashahuriyar 'yar kasuwa - Jaruma Rayya
Ba ni da burin da ya wuce in zama mashahuriyar 'yar kasuwa - Jaruma Rayya. Hoto daga @officialSurayya
Asali: Twitter

KU KARANTA: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

A wani labari na daban, fitaccen mawakin Hausa Nazifi Asnanic ya bayyana wa BBC cewa cikin tarihin wakokin da ya rera, ba zai taba mantawa da wakar da ya yi wa Goodluck Jonathan, tsohon shugaban kasar Najeriya ba.

Duk da dai mawakin ya ce ya fi kaunar wakar da ya yi wa Dr Rabiu Musa Kwankwaso, amma ya ce wacce ya yi wa Jonathan ta matukar tsaya masa a rai sakamakon halin da ya fada bayan nan.

Fitaccen mawakin ya sanar da hakan ne a hirar da yayi da BBC kai tsaye a shafinsu na Instagram.

Kamar yadda yace, ya rera wa Jonathan waka ta yi karfi amma sai shekarar 2015 ta iso kuma "Masu son Buhari sun taru sun yi min yawa."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel