NAHCON ta yi karin haske a kan yiwuwar yadda za a gudanar da aikin Hajin bana
Zikrullah Kunle Hassan, shugaban hukumar jin dadin alhazai ta kasa (NAHCON), ya ce mai yiwuwa kasar Saudiyya ta dakatar da wasu kasashe daga halartar aikin Hajjin bana.
Idan hakan ta tabbata, kasashen da hukuncin zai shafa sune wadanda aka samu tsanantar annobar cutar korona.
Ya bayyana hakan ne yayin wani taro mai taken "makomar aikin Hajj da Umrah bayan annoba", wanda kungiyar masu ruwa da tsaki a aikin Hajji da Umrah a Najeriya suka shirya.
An gudanar da taron ne a manhajar Zoom da ke yanar gizo.
A cikin wani jawabi da Mousa Ubandawaki, mataimakin darektan yada labarai a NAHCON, ya fitar, shugaban hukumar ya bayyana cewa mai yiwuwa gwamnatin kasar Saudiyya ta zo da sabbin tsaraba yayin aikin Hajjin bana.
Ya kara da cewa mahukuntan kasar za su yi hakan ne domin ganin an takaita yaduwar kwayar cutar korona yayin aikin Hajjin bana.
A cewarsa, mai yiwuwa kasar Saudiyya ta dauki karin wasu matakan ma su tsauri idan har za a yi aikin Hajjin bana.
Ya ce irin wadannan matakai sun hada da rage adadin maniyyata daga kasashe, dakatar da maniyyata daga kasashen da annobar korona ta tsananta, hana maniyyata dattijai da marasa koshin lafiya samun biza.
DUBA WANNAN: An kama matashi mai shekaru 25 ya na yi wa dattijuwa mai shekaru 85 fyade a karamar hukumar Rafi
Zikrullah, wanda shine jagoran tattaunawa yayin taron, ya bayyana karfin gwuiwar cewar za a gudanar da aikin Hajjin bana duk da rashin tabbas saboda barkewar annobar korona.
"Kasar Saudiyya ce kadai take da ikon yanke shawara. Za mu iya yanke ta mu shawarar ne kawai bayan sun yanke tasu," a cewarsa.
Ya kara da cewa, "na tabbata ko za a yi aikin Hajjin zai zo da sabbin sharudai. Ba zata zama tamkar sauran aikin Hajji da aka saba ba. Za a binciki lafiyar mutane sosai, za a killace wasu ma.
"Sannan za a bukaci yin amfani da tsarin nesanta yayin gudanar da aiyukan ibada da zirga - zirga."
A cikin watan Fabrairu na shekarar nan ne kasar saudiyya ta sanar da dakatar da bayar da takardun bizar ziyartar kasa domin gudanar da aikin Umrah.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng