Yanzu-yanzu: Buhari ya zabi Okonjo-Iweala don rike mukamin shugabar WTO

Yanzu-yanzu: Buhari ya zabi Okonjo-Iweala don rike mukamin shugabar WTO

- Shugaba Muhammadu Buhari ya yi na'am da nadin Ngozi Okonjo Iweala, a matsayin darakta janar ta kungiyar cinikayya ta duniya (WTO)

- Buhari ya janye takarar Yonov Fredrick Agah, wakilin dindindin na Najeriya a WTO, a matsayin

- Za a gudanar da zaben a Geneva da ke Switzerland a shekarar 2021, mukamin da za a rike na shekaru hudu daga 2021 zuwa 2015

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Ngozi Okonjo Iweala, a matsayin darakta janar ta kungiyar cinikayya ta duniya (WTO), The Cable ta ruwaito.

Kamar yadda takardar da jaridar The Cable ta gani a ranar Alhamis, Buhari ya janye takarar Yonov Fredrick Agah, wakilin dindindin na Najeriya a WTO, a matsayin.

Yanzu-yanzu: Buhari ya zabi Okonjo-Iweala don rike shugaban WTO
Yanzu-yanzu: Buhari ya zabi Okonjo-Iweala don rike shugaban WTO Hoto: YellowDanfo
Asali: Twitter

Za a yi zaben a Geneva da ke Switzerland a shekarar 2021, mukamin da za a rike na shekaru hudu daga 2021 zuwa 2015.

KU KARANTA KUMA: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce Najeriya za ta tsaya tsayin daka wajen goyon bayan Dakta Akinwumi Adesina a kokarin sa na sake zama shugaban bankin ci gaban Afirka, AfDB.

Hakan ya fito ne daga bakin mai ba shugaban kasa shawara ta musamman kan harkokin yada labarai, Mista Femi Adesina.

Cikin sanarwar da Mista Femi ya gabatar, ya ce Buhari ya bayar da tabbacin ne a fadarsa ta Abuja, a ranar Talata yayin da ya karbi bakuncin Dr Adesina wanda ya kai masa ziyarar ban girma.

Buhari ya yi alkawarin cewa, Najeriya za ta hada kai tare da sauran shugabanni da masu ruwa da tsaki a bankin AfDB don ganin an sake zabar Dakta Adesina a wa’adi na biyu.

Shugaban kasar ya ce zai yi hakan ne duba da tubalin nasarorin da Dakta Adesina ya kafa a wa'adin mulkinsa na farko.

KU KARANTA KUMA: Cikin gaggawa: An tafi da mahaifin gwamnan Nasarawa asibiti, an yi wa fadarsa feshi

Ya tunasar da Dakta Adesina rawar da ya taka wadda ta tabbatar da nasararsa ta kasancewa shugaban bankin AfDB (African Development Bank).

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel