Kakakin hukumar kula da gidajen gyaran hali ya yi magana a kan hallayar Orji Kalu lokacin da ya ke kurkuku

Kakakin hukumar kula da gidajen gyaran hali ya yi magana a kan hallayar Orji Kalu lokacin da ya ke kurkuku

- An sallami tsohon gwamnan jihar Abia, Orji Uzor Kalu, daga gidan yarin Kuje da ke Abuja

- An shafe fiye da shekaru 10 ana shari'a a kan tuhumar da EFCC ke yi wa Kalu na tafka badakala da dukiyar jama'a lokacin da ya ke gwamna

- Kalu ya shafe watanni 6 kacal a gidan yari kafin kotun koli ta warware hukuncin da aka zartar a kansa

Kakakin hukumar kula da gidajen gyaran hali ya ce Orji Uzor Kalu, bulaliyar majalisar dattijai, ya kasance mai kyakyawan hali yayin da ya ke gidan yarin na Kuje da ke Abuja.

Da ya ke magana da jaridar TheCable ranar Alhamis, Austin Njoku, kakakin hukumar, ya ce basu taba samun wata matsala da Kalu ba a tsawon zamansa a gidan yarin.

"Ka na tsammani mutum mai kima kamarsa zai haddasa fitina? zai yi fada saboda abinci ne? ya kasance mai biyayya ga dokoki da tsare - tsaren gidan yari," a cewar Njoku.

Sanna ya kara da cewa, "ba mu taba samun wata matsala da shi ba a tsawon zamansa na wata shida a gidan yari."

An yankewa Kalu hukuncin daurin shekaru 12 a watan Disamba na shekarar 2019 bayan an gurfanar da shi a gaban kotu da laifin karkatar da biliyan N7.1 daga asusun gwamnatin jihar Abia a lokacin mulkinsa.

Kakakin hukumar kula da gidajen gyaran hali ya yi magana a kan hallayar Orji Kalu lokacin da ya ke kurkuku
Orji Kalu lokacin da ya ke barin kurkuku
Asali: UGC

Hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arziki (EFCC) ta gurfanar da Kalu da Ude Jones Udeogu, tsohon darektan kudi da asusu na jihar Abia, bisa tuhumarsu da laifuka 36 ma su nasaba da cin hanci.

DUBA WANNAN: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

A ranar 8 ga watan Mayu ne kotun koli ta soke hukuncin da aka zartar a kan Udeogu bisa hujjar cewa alkalin da ya yanke mu su hukunci bashi da hurumin sauraron kararsu bayan daga darajarsa zuwa alkalin kotun daukaka kara.

An saki Kalu wata guda bayan fitar Udeogu daga gidan yari.

Kafin kotun koli ta warware hukuncin da aka yanke ma sa, Kalu ne gwamna na uku da kotu ta tura gidan yari bayan samunsu da laifin almundahana.

Har yanzu sauran gwamnonin biyu; Joshua Dariye, tsohon gwamnan jihar Filato, da takwaransa na jihar Taraba, Rabaran Jolly Nyame, su na gidan yarin Kuje.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel