Rayuka 3 na taba kashe ba 16 ba - Shahararren dan kungiyar asiri ya yi bayani

Rayuka 3 na taba kashe ba 16 ba - Shahararren dan kungiyar asiri ya yi bayani

Rundunar 'yan sandan jihar Ogun a ranar Talata ta damke wani shahararren dan kungiyar asiri mai suna Adewale Adeoye.

Adeoye wanda aka fi sani da '16' a kungiyarsu, ya ce mutum uku kacal ya kashe tun bayan da ya shiga kungiyar.

An damke wasu masu laifin 30 inda aka mika su ofishin 'yan sanda da ke Eleweran a garin Abeukuta.

Laifukansu sun kama daga kungiyar asiri, fashi da makami da mallakar miyagun makamai, kwamishinan 'yan sandan jihar, Kenneth Ebrimson ya sanar.

Rayuka 3 na taba kashe ba 16 ba - Shahararren dan kungiyar asiri ya yi bayani
Rayuka 3 na taba kashe ba 16 ba - Shahararren dan kungiyar asiri ya yi bayani Hoto: The Nation
Asali: UGC

Ebrimson ya ce jami'an 'yan sanda ne suka kama masu laifin a sassa daban-daban na jihar a watan da ya gabata.

KU KARANTA KUMA: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

Kamar yadda jaridar The Nation ta bayyana, Adeoye ya kasance a jerin mutanen da 'yan sandan ke nema ido rufe sakamakon kashe-kashen da 'yan kungiyar asiri ke yi a yankin Ijebu-Ode da kewaye.

Ya kara da cewa, an damke Adeoye tare da wasu mutum biyar a maboyarsu da ke Ijebu-Ode a watan Mayu.

Ebrimson ya ce an samu bindiga kirar fiston guda biyu, harsasai 11, wiwi da kuma layu a tare da su.

A yayin zantawa da manema labarai, Adeoye ya amsa laifinsa. Ya ce mutum uku kacal ya taba kashewa tun bayan shigarsa kungiyar asiri.

Ya yi ikirarin cewa, biyu daga cikin mutanen da ya kashe sune makasan shugaban Ijebu-Ode.

Adeoye ya bayyana sunan wadanda ya kashe a matsayin Vandan, Koledowo da Abbas.

Ya ce sau biyu ana gurfanar da shi a gaban kotu a tsakanin 2012 zuwa 2017.

A yayin da aka tambaye shi ko ya bar kungiyar bayan kama shi da aka yi, Adeoye ya ce, "Ban fita daga kungiyar ba. Ba su bani dama ba saboda sun ce za su kashe ni idan na bar kungiyar."

KU KARANTA KUMA: COVID-19: Gwamnan Kogi ya yi watsi da rahoton NCDC

A wani labarin kuma 'Yan sanda sun kama wani matashi, Ishaku mai shekaru 21 da haihuwa saboda kashe abokinsa, Zeloti ta hanyar daba masa wuka don rikici a kan budurwa.

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a wani mashaya a garin Dass a ranar Juma'a 29 ga watan Mayu inda Ishaku ya caka wa Zeloti wuka har sau uku kan musun da suke yi a kan wanene ainihin saurayin yarinyar.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Bauchi, DSP Ahmed Wakili ya tabbatar da afkuwar lamarin kamar yadda LIB ta ruwaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel