Tuwita: Davido, Buhari da Atiku su na cikin wadanda su ka fi yawan Mabiya

Tuwita: Davido, Buhari da Atiku su na cikin wadanda su ka fi yawan Mabiya

Kamfanin StatiSense wanda su ka kware wajen bincike da nazarin alkaluma a Najeriya, sun bayyana mutanen da su ka fi kowa shahara a dandalin sada zumunta na Tuwita.

Mafi yawan wadannan mutane da su ka shiga cikin jeringiyar, fitattun ‘yan siyasa ne, da mawaka da kuma 'yan wasan kwaikwayo. Akwai kuma wasu gidajen jaridun da ake ji da su.

Ga wadanna mutane da yawan mabiyansu kamar yadda StatiSense ta fitar da rahoto a ranar 1 ga watan Yuni, 2020. Babu mamaki cewa zuwa yanzu adadin mabiyan sun canza.

1. Davido – Miliyan 7.11

2. Wiz Kid – Miliyan 6.55

3. Don Jazzy – Miliyan 4.66

4. Tiwa Savage – Miliyan 4.00

5. Gidan Channels TV – Miliyan 3.84

6. Burna Boy – Miliyan 3.38

7. Olamide – Miliyan 3.22

8. Jaridar Punch – Miliyan 3.22

9. D Banj – Miliyan 3.20

10. Shugaban kasa Buhari – Miliyan 3.12

KU KARANTA: Yadda 'Yan Majalisa da tsofaffin Shugabanni ke tashi da Tiriliyoyin kudi

A cikin wadanda su ka samu shiga sahun goman farko, shugaban kasa Muhammadu Buhari ne kadai ‘dan siyasa. Taurarin mawaka bakwai da gidajen jarida biyu su ka rufe wannan jeri.

11. Banky W – Miliyan 2.97

12. Jaridar Sahara Reporters – 2.95

13. Atiku Abubakar – Miliyan 2.87

14. 2 Face (2Baba) – Miliyan 2.84

15. Yemi Osinbajo – Miliyan 2.71

A wannan sahu ne aka samu mataimakin shugaban kasa mai-ci watau Farfesa Yemi Osinbajo da kuma tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar tare da wasu manyan mawaka.

16. Peter P Square – Miliyan 2.69

17. Ice Prince – Miliyan 2.56

18. Jaridar Vanguard – Miliyan 2.55

19. Simi – Miliyan 2.37

20. Genevieve Nnaji – Miliyan 2.20

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel