Boko Haram: 'Yan ta'adda sun yi garkuwa da ma'aikatan jin kai 3 da soja 1

Boko Haram: 'Yan ta'adda sun yi garkuwa da ma'aikatan jin kai 3 da soja 1

Mayakan Boko Haram sun yi garkuwa da mutane hudu da suka hada da ma'aikatan jin kai uku da soja daya a kan babbar hanyar Monguno zuwa Maiduguri, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

An gano cewa al'amarin ya faru wurin karfe 11:30 na safiyar Talata a karamar hukumar Guzamala da ke kan babbar hanyar Maiduguri.

Cibiyar taimakon gaggawa ta jihar (SEMA) ta tabbatar da garkuwa da aka yi da ma'aikacin ta.

Wani jami'in SEMA wanda ya bukaci a boye sunansa ya ce an yi garkuwa da ma'aikacin su da yake aiki a matsayin manajan sansani a garin Monguno.

"Tabbas mun samu labarin aukuwar mummunan lamarin a ranar Talata tsakanin Monguno da Maiduguri.

"Mun gano cewa mutane hudu mayakan Boko Haram suka sace, jami'in SEMA daya, ma'aikacin NGO daya da soja daya. Muna matukar alhini," majiyar daga SEMA tace.

Shugaban hukumar SEMA, Hajiya Ya'bawa Kolo, wacce ta tabbatar wa jaridar Daily Trust, ta ce cibiyar ta kai wa jami'an tsaro korafi.

KU KARANTA: Zulum ya sallami dukkan ma'aikatan babban asibitin Ngala da ke Borno (Hotuna)

"Eh, mun kai wa 'yan sanda rahoto kuma suna amfani da bayanan da direban motar ya bada don tallafawa. Muna kokari tare da addu'ar ganin an sakesu," tace.

Hakazalika, kungiyar taimakon kai da kai da aka yi garkuwa da ma'aikatanta biyu, ta tabbatar da aukuwar lamarin.

Amma da aka tuntubi mai magana da yawun rundunar sojin, Kanal Sagir Musa ya sanar da Daily Trust cewa bai san da aukuwar lamarin ba.

A wani labari na daban, hedkwatar tsaro ta kasa da ke Abuja, ta ce rundunar sojin Operation Lafiya Dole ta gano cewa mayakan Boko Haram da ke yankin Isari a karamar hukumar Gamboru Ngala sun haka ramuka.

A ranar Litinin, rundunar sojin ta tabbatar da cewa ta bankado ramuka da aka haka da kyau a kauyukan Gulwa, Diime, Musiri, Wuri Bari, Mada, Sangaya, Jarawa, Mutu, Isari da Mudu a karamar hukumar.

A wata takarda da fannin yada labaran dakarun ta fitar, ta ce wasu daga cikin manyan mayakan Boko Haram din sun mika kansu kuma an karbesu, The Punch ta ruwaito.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel