An kama matashin da ya kashe kaninsa saboda farfesun kayan ciki

An kama matashin da ya kashe kaninsa saboda farfesun kayan ciki

Rundunar 'yan sandan jihar Ebonyi ta damke wani mutum sakamakon zarginsa da ake da kashe dan uwansa mai shekaru 20 mai suna Ebubechi Orogwu.

Rahotanni sun bayyana cewa, wanda ake zargin mai suna Chinwekpe Orogwu ya kashe Ebubechi ne saboda ya ci mishi farfesun kayan cikin akuyarsa.

Lamarin ya faru a ranar 15 ga watan Mayun 2020 a Amauda Nzashi Ndufu Echara da ke karamar hukumar Ikwo ta jihar Ebonyi, kamar yadda The Nation ta wallafa.

An gano cewa, an yanka akuyar ne a gidan su amma kason kayan cikin sai ya fada kan Chinwekpe da dan uwansa.

An gano cewa 'yan uwan biyu na morar farfesun kayan cikin, yayin da Chinwekpe ya zargi Ebubechi da cin nashi kason.

Yayin musu a kan hakan, Chinwekpe ya samu katon katako wanda yayi amfani da shi wurin buga wa kaninsa a kai.

Rahotanni sun bayyana cewa, ihun kanin ne yasa makwabta suka gaggauta fitowa don ganin abinda ke faruwa.

A take kuwa ya fadi, amma sai aka kwashe shi zuwa asibitin koyarwa na Alex Ekwueme da ke Abakaliki inda aka tabbatar da mutuwarsa.

A kan farfesun kayan ciki: 'Yan sanda sun damke matashin da ya halaka kaninsa
A kan farfesun kayan ciki: 'Yan sanda sun damke matashin da ya halaka kaninsa. Hoto daga The Nation
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Gwamnatin Katsina ta yi martani kan kisar hakimin 'Yantumaki

Gawar Ebubechi na nan a Ikwo inda aka mika ta ma'adanar gawawwaki da ke babban asibitin Ikwo.

A yayin zantawa da manema labarai a Abakaliki, kakakin rundunar 'yan sandan jihar, DSP Loveth Odah, ta tabbatar da aukuwar lamarin tare da kama wanda ake zargi.

Ta ce an kaiwa 'yan sanda rahoton aukuwar lamarin daga yankinsu mamacin.

Odah ta ce wani mutum mai suna Clement Nwofia ne ya kai rahoton.

Ta ce Nwofia ya jaddada cewa, Chinwekpe ya yi amfani da katako ne wajen buga wa Orogwu Ebubechi mai shekaru 20, a kai.

"Wanda ake zargin ya yi ikirarin cewa mamacin ya cinye mishi kayan cikin akuyar.

"A halin yanzu ana bincikar al'amarin amma gaskiya akwai abun mamaki idan aka ce saboda akuya ne aka kashe mutum," Odah ta jaddada.

A wani labari na daban, a ranar Talata, gwamnatin tarayya ta bai wa 'yan Najeriya shawara a kan zuwa wurin bauta. Ta ce matukar mutum ya kai shekaru 55 zuwa sama, toh ya guji zuwa masallatai da majami'u.

Masu ciwuka kamar ciwon sukari, daji, kanjamau da sauran su, duk ana bukatar su da yin hakurin bauta a gidajensu, gwamnatin ta kara da cewa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel