Mai laifi ya jagoranci 'yan sanda zuwa wurin da su ka binne gawar lauyan da su ka kashe
Rundunar 'yan sanda a jihar Edo ta tono gawar lauyan nan, Mista Omon Iyoha Osobase, wanda wasu gungun 'yan daba su ka kashe yayin da ya ke kokarin rabasu fada a farkon watan Mayu.
Lamarin ya faru ne a wani wurin shakatawa a Benin, babban birnin jihar Edo, inda matasan su ka lakadawa Osobase mugun duka tare da tafiya da shi a motarsu.
Rundunar 'yan sanda ta ce ta kama wasu daga cikin wadanda ake zargi da kisan lauyan, sannan ta kara da cewa wadanda ake zargin sun jagoranci tawagar 'yan sanda zuwa wurin da su ka binne Osobase.
Wasu kwararru ne daga babban asibitin birnin Benin su ka tono gawar Osobase tare da tafiya da ita zuwa asibiti domin gudanar da bincike.
A jiya, Talata, ne Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya aika sakon ta'aziyya ga dangin matashiyar dalibar nan, Uwaila Omozuwa, wacce aka kashe ta hanyar yi ma ta fyade a cikin coci a jihar Edo.
A takaitaccen sakon da ya wallafa a shafinsa na tuwita, shugaba Buhari ya bukaci rundunar 'yan sanda ta gaggauta gudanar da bincike tare da zakulo wadanda su ka yi wa matashiyar kisan gilla.
DUBA WANNAN: Sulhu da 'yan bindiga: Masari ya bayyana wadanda su ka ci amanar gwamnatinsa
"Ina mai mika sakon ta'aziyya ga dangi da abokan Uwaila Omozuwa. Ina kira ga rundunar 'yan sanda ta Najeriya a kan ta hanzarta yin bincike tare da zakulo duk wani mai hannu a cikin lamarin domin tabbatar da cewa an gurfanar da su a gaban shari'a," a cewar shugaba Buhari.
Rundunar 'yan sandan Najeriya a jihar Edo ta sanar da cewa ta kama wani da ake zargin ya na da hannu a kisan Omozuwa.
A cewar Chidi Nwabuzor, kakakin rundunar 'yan sandan jihar Edo, an kama mutumin ne bayan zanen yatsunsa sun fito a jikin tukunyar gas da aka yi amfani da ita wajen kisan matashiyar.
Rundunar 'yan sanda ta ce an kaiwa Omozuwa farmaki ne yayin da ta ke karatu a cikin Cocin RCCG (Redeemed Christian Church of God), da ke birnin Benin.
Mai gadin Cocin ya samu matashiyar a kwance cikin jini, rabin jikinta tsirara yayin da ya zo aiki da daddare.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng