Shugaba Buhari ya yi na’am da baza Jami’an tsaro su yi gadin karafun sadarwa

Shugaba Buhari ya yi na’am da baza Jami’an tsaro su yi gadin karafun sadarwa

A ranar Talata, 2 ga watan Yuni, 2020 mu ka ji cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da bukatar bada tsaro wajen gadin karafun kamfanonin sadarwa a Najeriya.

Ma’aikatar sadarwa da tattalin arzikin zamani ta tabbatar da cewa shugaban kasa ya yi na’am da baza jami’an tsaro da nufin yin gadin duk wasu karafun sadarwa da ke fadin kasar nan.

Mai magana da yawun bakin mai girma ministan tarayyar, Uwa Suleiman ta bayyana wannan a wani jawabi da ta fitar a farkon makon nan a madadin Minista Isa Ali Ibrahim Pantami.

A jawabin hadimar ministar ta ce an sanar da ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan harkar tsaro da kuma hedikwatar rundunar sojojin Najeriya da hukumar NSCDC a kan matakin.

Haka zalika Sulaiman ta ce an sanar rundunar ‘yan sanda da jami’an tsaro masu fararen kaya na DSS game da wannan lamari domin su rika aiko dakaru da za su rika gadin arzikin kasar.

Karafunan sadarwa su na da matukar amfani wajen bada damar hawa shafukan yanar gizo da yin waya da aika sakonni, don haka ma’aikatar sadarwa ta na bukata a kara matakan tsaro.

KU KARANTA: Shugaba Buhari zai gyara kuskuren da aka yi a FCC - Shugaban Majalisa

A dalilin haka ne Isa Ali Ibrahim Pantami ya roki shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci jami’an tsaro su tsare karafunan da ke bada karfin sadarwa, kuma aka amince da bukatar.

A cewar ma’aikatar sadarwa da tattalin arzikin zamanin kasar, jami’an tsaro za su taimaka wajen maganin barayi da masu yi wa kamfanonin sadarwan ta’adi, sannan su kare ran jama’a.

Dr Isa Pantami ya yabawa kokarin da jami’an tsaro su ke yi a kasar kamar yadda Uwa Sulaiman ta bayyana. “Mu na duba yiwuwar tabbatar da umarnin shugaban kasar.” Inji Ministan.

Ministan ya bayyana cewa yayin da ake fama da annobar cutar COVID-19, mutane da-dama za su bukaci amfani da kafafin yada labarai na yanar gizo domin a ceci tattalin arzikin kasar.

A karshe, ma’aikatar ta tabbatar da cewa gwamnatin tarayya ta yi kira ga kamfanonin sadarwa da su kara rage farashin hawa shafin yanar gizo da kuma kudin yin waya ga ‘yan Najeriya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel