Bai kamata farashin mai ya haura N70 ba a yanzu - PDP

Bai kamata farashin mai ya haura N70 ba a yanzu - PDP

Babbar jam'iyyar adawa a Najeriya, PDP, ta kirayi gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, da ta daina tsawwala wa 'yan Najeriya kan tsadar da farashin man fetur ya yi.

PDP ta bukaci Buhari ya gaggauta rage farashin man fetur zuwa naira 70 duk lita, lamarin da ta ce haka shi ne zai haskaka dacewa da faduwar da farashinsa ya yi a kasuwar duniya.

Kakakin jam'iyyar na kasa, Kola Ologbondiyan, shi ne ya bayyana wannan bukata cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, 3 ga watan Yuni.

PDP yayin watsi da sabon farashin da gwamnatin tarayya ta sanar a ranar Litinin, ta ce sayar da litar mai naira 121 rashin adalci ne kawai irin na jam'iya mai mulki a kasar ta APC

Ta ce ko kadan gwamnatin Buhari ba ta la'akari da halin ni 'ya su da al'ummar kasar ke fuskanta, musamman a wannan lokaci da annobar cutar korona ta janyo karayar tattalin arziki.

Buhari da Kakakin jam'iyyar PDP na kasa; Kola Ologbondiyan
Buhari da Kakakin jam'iyyar PDP na kasa; Kola Ologbondiyan
Asali: UGC

A sanarwar da jam'iyyar PDP ta fitar, ta jaddada cewa, farashin naira 121 duk lita, ya nuna ana zaluntar 'yan Najeriya adadin kudin da ya haura naira hamsin a kowace litar mai daya.

Legit.ng Hausa ta ruwaito cewa, kungiyar manyan dillalan man fetur ta kasa (IPMAN), ta umarci dukkanin mambobinta da su fara siyar da makamashin man fetur a kan N123.50 duk lita daya.

Hakan ya biyo bayan shawarar rage farashin litar mai a fadin Najeriya daga Naira 125.00 zuwa Naira 121.50 da Gwamnatin Tarayya ta yi.

KARANTA KUMA: Sharaɗi 15 da Gwamnatin Tarayya ta shata wa wuraren bauta a Najeriya

Hukumar daidaita farashin man fetur PPPRA ce ta sanar da rage farashin man fetur cikin wasikar da ta aikewa 'yan kasuwar mai a ranar Lahadi, 31 ga Mayu, 2020.

Da ya ke jawabi dangane da lamarin, shugaban kungiyar IPMAN reshen jihar Kano, Bashir Dan-Mallam, ya ce za su dauki shawarar wannan sabon hukunci da PPPRA ta fitar.

A yayin da Hukumar kayyade farashin da ba da shawarar a koma siyar da litar mai daya a kan N121.50 ko kuma N123.50, Dan-Mallam ya ce za su rika siyar da kowace lita daya a kan N123.50.

Sai dai fa ya ce al'umma su sani cewa, wannan kayyade sabon farashi da aka yi a yanzu ba umarni bane, illa iyaka shawara da suka ga za su iya dauka.

A sanadiyar haka Dan-Mallam ya nemi dukkan dillalai da ke karkashin jagorancinsa, da su yi riko da sabon farashin, kuma su koma siyar da kowace lita daya a kan Naira 123 da kobo hamsin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel