Yanzu-yanzu: 'Yan bindiga sun kashe mutum 9 sabon harin Kaduna

Yanzu-yanzu: 'Yan bindiga sun kashe mutum 9 sabon harin Kaduna

A kalla mutum tara ne suka rasa rayukansu yayin da wasu suka raunata bayan harin da 'yan bindiga suka kai kauyen Avong Doka a karamar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna.

Wannan al'amarin ya faru bayan mako daya da 'yan bindiga suka kone gidaje a wurin kiwo da ke kauyen Agwala Dutse, da ke karamar hukumar Kajuru.

Duk da hukumar 'yan sanda a Kaduna basu tabbatar da aukuwar lamarin ba, shugaban karamar hukumar Kajuru, Cafra Caino ya sanar da Channels TV cewa 'yan bindiga sun kutsa kauyen a sa'o'in farko na yau Laraba.

Sun dinga harbe-harbe, lamarin da yasa mazauna kauyen suka fara neman mafaka.

Ya ce mutum tara ne suka mutu a take, sakamakon raunikan da suka samu sakamakon harbin.

Wasu mazauna yankin sun samu miyagun raunika kuma an mika su asibiti don samun taimakon gaggawa.

Shugaban karamar hukumar ya ce ba don isowar sojoji ba, da al'amarin ya fi haka.

Ya kara da cewa, sojojin sun nemi wurin zama a kauyen bayan sun fatattaki 'yan bindigar.

Yanzu-yanzu: 'Yan bindiga sun kashe mutum 9 sabon harin Kaduna
Yanzu-yanzu: 'Yan bindiga sun kashe mutum 9 sabon harin Kaduna. Hoto daga The Punch
Asali: Facebook

KU KARANTA: Nasara daga Allah: Babban asirin Boko Haram ya tonu a Borno - DHQ

A wani labari na daban, sabuwar dokar kulle ta Ingila ga 'yan kasa ta haramta jima'i da dan waje wanda ba dan gida ba a yayin da gari yake kulle.

A ranar Litinin, 1 ga watan Yunin 2020, gwamnatin Ingila ta bayyana sabuwar dokarta da ta haramta shakatawa da jama'a da ba na gida ba a yayin da dokar kulle ke aiki.

Sabuwar dokar ta ce: "Babu wanda aka amince ya yi wani taro a waje ko a gida wanda ya kai mutum biyu ko fiye."

Da farko, duk wanda ya shiga gidan wani ya take dokar kullen shi ake hukuntawa. Amma a halin yanzu da wanda ya shiga, da wanda aka shigarwa gida duk za a gurfanar dasu tare da hukunta su.

Kamar yadda sabbin dokokin suka bayyana, masu dalili mai karfi ne za a bari su yi taro a cikin gida amma banda saduwa a tsakani.

Dalilan sun hada da motsa jiki, kaiwa da kawowar jama'a da kuma masu ayyukan dole.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel