FG ta bayyana rukunin mutanen da aka haramtawa zuwa masallatai da majami'u

FG ta bayyana rukunin mutanen da aka haramtawa zuwa masallatai da majami'u

A ranar Talata, gwamnatin tarayya ta bai wa 'yan Najeriya shawara a kan zuwa wurin bauta. Ta ce matukar mutum ya kai shekaru 55 zuwa sama, toh ya guji zuwa masallatai da majami'u.

Masu ciwuka kamar ciwon sukari, daji, kanjamau da sauran su, duk ana bukatar su da yin hakurin bauta a gidajensu, gwamnatin ta kara da cewa.

Ta ce wannan shawarar ta zama dole domin kuwa an gano cewa a wuraren bauta ne ake yada annobar da ta gallabi duniya.

Gwamnatin tarayyar ta sanar da wannan ne ta bakin kwamitin fadar shugaban kasa na yaki da annobar korona.

Ta bada tsare-tsare ga jihohi na yadda za su tattauna da shugabannin addinai kafin bude majami'u da masallatai.

Gwamnatin ta ce tsare-tsaren da ta bada, bata so wata gwamnatin jiha ta sassauta a kansu yayin kaiwa matsaya da shugabannin addinan.

'Yan Najeriya sun takura gwamnati a kan bude wuraren bauta duk da kuwa hauhawar masu cutar korona da ake samu, jaridar The Nation ta wallafa.

Shugaban PTF, Dr Aliyu Sani, wanda ya sanar da tsare-tsaren, ya ce dole ne wuraren bauta su dinga rubuta sunayen masu bauta.

Dr Sani ya ce, hakan ce za ta sa a zakulo masu cutar cikin sauki koda kuwa sun je wurin bauta, wanda ba a fatan hakan.

Idan shekarunka sun kai 55 zuwa sama kada ka je wurin bauta - PTF
Idan shekarunka sun kai 55 zuwa sama kada ka je wurin bauta - PTF. Hoto daga The Nation
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Mataimakin gwamnan Bauchi ya harbu da korona

Ya yi kira ga masu bauta da ke fuskantar alamomin COVID-19 da su guji zuwa masallatai da majami'u.

Ya ce: "Muna shawartar masu wasu cutuka na daban da babbar murya kamar su ciwon sukari, ciwukan zuciya, kanjamau, daji da wadanda suka zarta shekaru 55 da su zauna a gida.

"Idan muka dubi wadanda suka mutu sakamakon cutar, za mu gano cewa rabi daga cikinsu na da shekaru 50 ne zuwa sama.

"Kada ku je wurin bauta matukar kuka san kuna dauke da wata alama ta cutar. Alamun sun hada da zazzabi, tari, sarkewar numfashi ko kuma ka yi mu'amala da mai cutar a cikin makonni biyu.

"Duk mai bautar da aka gani da zazzabi ko wata alamar cutar, kada a bar shi shiga cikin jama'a."

Ya kara da cewa, "Ya kamata wuraren bauta su ajiye sunayen masu zuwa bauta da adireshinsu don zakulo masu cutar da wadanda suka yi mu'amala da su.

"Ganin yadda annobar nan ke ci gaba da yaduwa, muna shawartar malaman addinai da su guji kai ziyara gidajen mutane don addu'a."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164