Yanzu-yanzu: Mataimakin gwamnan Bauchi ya harbu da korona

Yanzu-yanzu: Mataimakin gwamnan Bauchi ya harbu da korona

Mataimakin gwamnan jihar Bauchi, Baba Tela ya kamu da cutar COVID-19 wadda aka fi sani da korona.

Babban mai taimakawa gwamnan Bauchi a fanin watsa labarai, Mukhtar Gidado ne ya sanar da hakan cikin sanarwar da ya raba wa manema labarai a Bauchi a ranar Laraba.

Ya ce an tabbatar da hakan ne bayan gwajin da Hukumar NCDC ta yi masa sakamakon alamomin cutar da suka bayyana a jikinsa.

Mr Gidado wanda shine shugaban kwamitin yaki da Korona da Zazzabin Lassa tuni ya killace kansa kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Yanzu-yanzu: Mataimakin gwamnan Bauchi ya harbu da korona
Yanzu-yanzu: Mataimakin gwamnan Bauchi ya harbu da korona. Hoto daga The Punch
Asali: Twitter

Ya ce, "Ana sanar da alumma cewa mai girma Sanata Baba Tela, mataimakin gwamnan jihar Bauchi kuma shugaban kwamitin yaki da COVID-19 ya kamu da coronavirus.

DUBA WANNAN: Kotu ta tsare mutumin da ya yi zina da surukarsa

"Ya kamu da cutar ne a lokacin da ya ke gudanar da aikinsa na jagorancin kwamitin yaki da cutar.

"Saboda haka, mai girma, Baba Tela ya killace kansa a Bauchi kuma kwararrun maaikatan lafiya suna bashi kulawa."

Hadimin gwamnan ya ce Hukumar NCDC ta dauki samfuri daga dukkan hadimansa na kusa da suke hulda kuma an bukaci su killace kansu yayin da suke dakon sakamakon gwajin.

Ya ce gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ya roki mutane su taya mataimakinsa da sauran wadanda ke fama da cutar da adduar samun waraka cikin kankanin lokaci.

"Gwamnan ya kuma yi kira ga mutanen jihar su cigaba da kiyaye dokokin da hukumomin lafiya suka bayar domin dakile yaduwar cutar a jihar," in ji shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel