Dan sanda ya kashe mutum a kan cin hancin N100

Dan sanda ya kashe mutum a kan cin hancin N100

Jami'in dan sanda ya harbe matashi mai shekaru 20 a duniya da ke kan babur din haya bayan ya kasa bashi N100.

Mazauna yankin sun ce, sai da dan sanda ya saita matashin mai suna Arabo Dauda sannan ya sakar masa harsashi, a wurin duba matafiya da ke garin maiha.

Lamarin ya haddasa hargitsi a yankin, bayan da matasa suka fara zanga-zanga tare da barazanar kai hari ofishin 'yan sandan yankin.

Har a halin yanzu ba a samu damar zantawa da kakakin rundunar 'yan sandan jihar Adamawa ba, DSP Sulaiman Nguroje.

Amma kuma, shugaban karamar hukumar Maiha, Idi Amin, ya tabbatar da aukuwar lamarin ga manema labarai.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, shugaban karamar hukumar ya tabbatar da cewa tuni ya sanar da gwamnan jihar tare da shugabannin tsaro.

A halin yanzu, ana kokarin bincikowa tare da damke wanda ya aikata laifin.

"Na samu kiran gaggawa a jiya a kan cewa dan sanda ya harbe matashi mai shekaru 20 a wurin duba matafiya da ke garin Maiha.

"Bayan tambayar mafarin lamarin, na gano cewa matashin ya hana dan sandan cin hancin N100 ne kacal," yace.

"Ya harbe matashin ne ta baya a yayin da ya juya tafiya gida daga siyan fetur da ya je. Hakan ce tayi sanadin mutuwar matashin," ya kara da cewa.

"An sake sanar da ni cewa dan sandan ya saba tilasta matafiya da ke kan hanyar bada N100 ta dole kafin ya bar su wucewa," shugaban karamar hukumar ya sanar.

Tirkashi: Dan sanda ya kashe mutum a kan cin hancin N100
Tirkashi: Dan sanda ya kashe mutum a kan cin hancin N100. Hoto daga The Nation
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Allah ya yi wa shugaban ƙaramar hukuma rasuwa

A wani labari na daban, wasu 'yan bindiga da ba san ko su wanene ba sun harbe hakimin 'Yantumaki har lahira a jihar Katsina, Abubakar Atiku Maidabino a fadarsa a safiyar ranar Litinin.

Wata majiya daga garin ta shaidawa Daily Trust cewa 'yan bindigan sun taho a babura ne misalin karfe 12 na dare inda suka rika harbe harbe a iska domin razana mutanen kauyen.

Daga bisani yan bindigan sun shiga cikin fadar suka kashe hakimin nan take kuma suka raunata daya daga cikin masu gadinsa.

Za a yi janai'zar mammacin misalin karfe 11 na safe a fadarsa bisa koyarwan addinin musulunci.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel