Allah ya yi wa shugaban ƙaramar hukuma rasuwa

Allah ya yi wa shugaban ƙaramar hukuma rasuwa

- Dr. Augustine Arogundade, zababben shugaban karamar hukumar Agbado/Oke-Ado da ke jihar Legas ya rasu

- Kamar yadda Omolola Essien ta fitar a wata takarda, ta ce shugaban karamar hukumar ya rasu a yau Talata da rana

- Ta yi addau'ar rahama gareshi da kuma hakuri ga iyalansa don jure wannan babban rashin da ya same su

Zababben shugaban karamar hukumar Agbado/Oke-Odo, Dr. Augustine Arogundade ya rasu.

Shugaban karamar hukumar ya rasu ne yau Talata 2 ga watan Yunin 2020 da rana, jaridar The Nation ta wallafa.

An tabbatar da mutuwar ne a wata takarda da shugabar Conference 57 ta jihar Legas, Omolola Essien ta fitar.

Ta yi fatan Ubangiji ya yafe wa shugaban karamar hukumar kura-kuransa tare da saka shi a gidan Aljanna.

Ta kara da yin kira ga jama'a da su yi wa iyalansa addu'a a wannan lokacin da suke fuskantar babbar jarabawa.

Yanzu-yanzu: Shugaban karamar hukuma ya riga mu gidan gaskiya
Yanzu-yanzu: Shugaban karamar hukuma ya riga mu gidan gaskiya. Hoto daga The Nation
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Kano: Har yanzu babu fita ranakun Litinin, Talata, Alhamis da Asabar — Ganduje

A wani rahoton, mun kawo muku cewa 'yan bindiga a ranar Asabar sun sace dan kasuwa, Yusuf Maifata a gidansa da ke garin Sankara da ke karamar hukumar Ringim ta jihar Jigawa.

Mazauna unguwar sun ce yan bindigan sun isa unguwar ne misalin karfe 1.47 na dare dauke da bindigu suna harbe harbe wadda hakan ya sa mutane suka firgita sannan suka sace Maifata daga gidansa.

Wani daga cikin iyalan dan kasuwar da ya nemi a sakaya sunansa ya ce, "Maifata ya dade yana fama da rashin lafiya.

An sallamo shi daga asibiti ranar Alhamis yana murmurewa a gida ne sai kwatsam abin ya faru.

Majiyar ya kuma bayyana cewa yan bindigan sun kira iyalansa sun nemi a biya su Naira miliyan 40 a matsayin kudin fansa.

Sun kuma tambayi irin abincin da dan kasuwan ya saba ci da magungunan da asibiti suka rubuta masa ya rika sha.

Yana sume suka tafi da shi saboda firgicin karar harbin bindiga da ya rika ji yayin da ya ke kwance a gadonsa kafin su shiga gidan su dauke shi kamar yadda majiyar ya shaidawa Premium Times.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel