Kisan daliba a coci: Fasto da kungiya mai zaman kanta sun saka kyauta mai tsoka ga wanda ya zo da bayani

Kisan daliba a coci: Fasto da kungiya mai zaman kanta sun saka kyauta mai tsoka ga wanda ya zo da bayani

- Apostle Johnson Suleman bayyana kokarin da yake wajen bankado makasan Vera Omozuwa

- Shugaban cocin Omega Fire Ministries ya ce zai bada kyautar naira miliyan daya ga duk wanda ya zo da bayani a kan makasan

- Fasto Suleman ya bayyana hakan ne a shafinsa na Twitter inda ya saka lambar da za a kira

- Har ila yau wata kungiyar mai zama kanta kuwa ta saka N500,000 ga duk wanda ya zo da wani bayani mai muhimmanci wanda zai kai ga fallasa makasan

Shugaban cocin Omega Fire Ministries, Apostle Johnson Suleman, ya bayyana kokarin da yake don tabbatar da adalci ga Vera Omozuwa.

Bayan fyade da kisan da aka yi wa dalibar a cikin wata coci, sanannen faston ya ce zai bada kyautar naira miliyan daya ga duk wanda ke da bayanai masu amfani a kan wadanda suka yi mugun aiki.

A wata wallafa da yayi a shafinsa na Twitter, ya rubuta: "Zan bada naira miliyan daya ga duk wanda yake da niyyar samar da bayani sahihi a kan fyade da kisan Vera Uwaila a coci... ku kira +2348119313785."

Daga wannan wallafar, za a iya cewa Apostle Suleman na bibiya tare da kokarin bankado makasan dalibar da ke shekarar farko a sashen karantar ilimin kananan halittu.

A daya daga cikin wallafarsa, faston ya kushe kisan kan tare da cewa ya za ta da gwamnan jihar don tabbatar da adalci a kan aika-aikar.

Ya jinjinawa shugaban makarantar, Benedicta Ehanire tare da bada tabbacin cewa za a bibiyi al'amarin.

Hakazalika, a jiya ne 'yan ajinsu da 'yan uwan mamaciyar suka yi zanga-zanga a gaban ofishin rundunar 'yan sanda da gidan gwamnatin jihar inda suka bukaci ayi bincike a kan mutuwarta.

KU KARANTA KUMA: Hotuna: Shugaban sojin saman Najeriya ya kai ziyara Sokoto

Wata kungiyar mai zama kanta kuwa ta saka N500,000 ga duk wanda ya zo da wani bayani mai muhimmanci wanda zai kai ga fallasa makasan, jaridar Vanguard ta ruwaito.

Amma kuma rundunar bincike ta 'yan sandan jihar Edo ta bayyana cewa: "Muna samun haske a binciken mu amma ba za mu ce komai ba har sai mun kammala."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel