Mai dakin Buhari ta bada gudumuwar kayan aiki da abinci domin yaki da COVID-19 a Nasarawa

Mai dakin Buhari ta bada gudumuwar kayan aiki da abinci domin yaki da COVID-19 a Nasarawa

– Uwargidar Najeriya ta gyara wani gini domin a rika kwantar da masu Coronavirus

– Aisha Muhammadu Buhari ta kuma bada wasu magungunan da za a ba masu ciwo

– Gidauniyar Matar shugaban kasar ta kuma raba kayan aiki da abinci ga Ma’aikata

Hajiya Aisha Muhammadu Buhari ta na cigaba da bada irin na ta gudumuwar wajen yaki da annobar cutar Coronavirus da ta addabi Najeriya da sauran kasashen a Duniya.

Matar Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta gyara wan gini ta yadda za a iya kwantar da masu fama da cutar COVID-19, bayan haka ta zuba wasu kayan aikin da za a bukata.

Uwargidar shugaban Najeriyar ta yi wannan kokari ne a babban asibitin Mararraba Gurku da ke jihar Nasarawa. Wannan wuri zai zama inda ake ajiye masu cutar Coronavirus.

Bayan wannan kokari da ta yi, Aisha Muhammadu Buhari ta raba kayan abinci ga likitocin da sauran malaman asibiti da su ka sadaukar da rayuwarsu domin ceto ran jama’a.

KU KARANTA: Aisha Buhari ta aikawa mutane motoci cike da kayan abinci

Buhari ta yi wannan aiki ne a karkashin gidauniyarta watau Future Assured. Mai dakin shugaban kasar ta bayyana wannan gagarumin aiki da ta yi ne a kan shafinta na Facebook jiya.

Daga cikin kayan aikin da aka rabawa malaman lafiyar akwai rigunan kariya na PPE da kuma wasu magunguna da masu jinyar cutar COVID-19 su ke bukata domin su murmure.

Bayan kwayoyin rage radadin ciwo, da kara karfin jiki da kwayoyin da ke taimakawa wadanda su ka gaza cin abinci, Aisha Muhammadu Buhari ta raba takunkumin N95 na rufe fuska

Kamar yadda Hajiya Aisha Muhammadu Buhari ta bayyana a shafin na ta, ta bada gudumuwar man wanke hannuwa, sannan ta raba abinci a matsayin tallafi ga ma’aikatan lafiya.

Daga cikin kayan abincin da mai dakin Muhammadu Buhari ta damkawa gwamnatin jihar Nasarawa akwai buhunan shinkafa da ta ce ta na sa ran za su taimakawa mutane.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng