Rigingimun APC: Abin da Buhari ya fada min yayin ganawarmu - Gwamna Obaseki

Rigingimun APC: Abin da Buhari ya fada min yayin ganawarmu - Gwamna Obaseki

A ranar Litinin ne gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, mai fama da rikicin cikin gida a jam'iyyar APC, ya ziyarci shugaban kasa, Muhammadu Buhari, domin gabatar ma sa da fom dinsa na sake neman takarar gwamna a karo na biyu.

Jim kadan bayan kammala ganwarsa da shugaba Buhari, Obaseki ya shaidawa manema labarai a fadar shugaban kasa cewa, "shugaba Buhari ya ba ni tabbacin samun goyon bayansa."

An dade ana nuna yatsa tare da musayar maganganu marasa dadi a tsakanin gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, da shugaban jam'iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole.

A yayin ziyarar, Obaseki ya shaidawa Buhari cewa mutanen jihar Edo su na goyon bayansa kuma a shirye su ke su sake zabensa.

Ziyarar da Obaseki ya kaiwa Buhari na zuwa ne a daidai lokacin da ya rage saura sati uku a gudanar da zaben fidda dan takarar jam'iyyar APC a zaben gwamnan jihar da za a yi a cikin watan Oktoba na shekarar nan.

Obaseki na fuskantar barazana daga Osagie Ize - Iyamu, tsohon dan takarar gwamna a jam'iyyar PDP da ake tunanin ya na da goyon bayan Oshiomhole; tsohon gwamnan Edo kuma tsohon shugaban kungiyar kwadago ta kasa (NLC).

Rigingimun APC: Abin da Buhari ya fada min yayin ganawarmu - Gwamna Obaseki
Yayin ziyarar da Obaseki ya kaiwa Buhari
Asali: Facebook

Da ya ke magana da manema labarai a fadar shugaban kasa, Obaseki ya ce ya kaiwa Buhari ziyara ne domin sanar da shi aniyarsa ta sake yin takarar kujerar gwamnan jihar Edo.

"Shugaban kasa ya karbeni hannu bibiyu, ya karramani sosai. Ya duba fom dina na takara da na nuna ma sa, ya yi min fatan alheri tare da bani tabbacin samun goyon bayansa," a cewar Obaseki.

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun budewa shugaban jam'iyyar APC wuta yayin da ya ziyarci kauyensu a Katsina

Ziyarar ta Obaseki na zuwa ne kwana daya kacal bayan ganawarsa da Tinubu da wasu sauran gwamnonin jam'iyyar APC a jihar Legas.

Tinubu ya kasance makusanci ga Oshiomhole, hasali ma shine ya kawo shi takarar kujerar shugabancin jam'iyyar APC bayan karewar wa'adin tsohon jam'iyyar, John Oyegun.

Taron na sirri, wanda aka yi ranar Lahadi, 31 ga watan Mayu, ya samu halartar shugaban kungiyar gwamnonin jam'iyyar APC, Atiku Bagudu na jihar Kebbi, gwaman jihar Ondo; Rotimi Akeredolu, gwamnan jihar Legas; Babajide Sanwo-Olu.

Ragowar sun hada da gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar GAnduje, Godwin Obaseki na jihar Edo, Simon Lalong na jihar Filato, Mai Mala Buni na jihar Yobe, Adeboyega Oyetola na jihar Osun, Badaru Abubakar na jihar Jigawa, da Abubakar Bello na jihar Neja.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel