Isa Pantami: Karfin GDP ya karu da 14% a kasar nan daga bangaren ICT

Isa Pantami: Karfin GDP ya karu da 14% a kasar nan daga bangaren ICT

Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Isa Ali Ibrahim Pantami ya ce bangaren ICT ya taimaka wajen bada gudumuwar 14.07% ga karfin tattalin arzikin Najeriya a farkon bana.

Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami ya ce ba a taba ganin irin wannan gudumuwa a alkaluman GDP na kasar ba a tarihi. Ministan ya bayyana wannan ta bakin hadiminsa, mista Femi Adeluyi.

A jawabin da ministan kasar ya fitar ranar Lahadi a babban birnin tarayya Abuja, ya ce ya yi farin cikin jin labarin cewa bangaren kimiyya na ICT ya bunkasa tattalin arzikin kasar a 2020.

A cikin makon jiya ne hukumar NBS mai tattara alkaluma a Najeriya ta fitar da rahoton tattalin arzikin kasar na farkon shekarar nan da ake ciki, rahoton ya nuna GDP ya karu da 1.87%.

“Ya kamata a sani cewa bangaren ICT ya ba GDP gudumuwar 14.07% a farkon 2020, wanda hakan ya zarce abin da aka samu na gudumuwar 13.32% a farkon shekarar da ta gabata.” inji sa.

KU KARANTA: Patami ya yi magana game da mutuwar Hadimin Shugaban kasa Abba Kyari

Ministan sadarwar ya ke cewa: “Ba a taba ganin irin wannan gudumuwa a tarihi ba.” Pantami ya ce sun yi nasara ne a dalilin irin kokarin da gwamnatin kasar ta ke yi.

Isa Ali Ibrahim Pantami ya bayyana wasu tsare-tsare da aka shigo da su a karkashin shugabancin Muhammadu Buhari a matsayin abubuwan da su ka taimaka wajen zaburar da bangaren.

A karshe, ministan tarayyar ya yi kira ga sauran bangarorin gwamnati su yi amfani da wannan dama da shugaba Buhari ya kawo wajen fadada amfanin da su ke yi da kimiyyar na ICT.

Kamar yadda hukumar dillacin labarai ta rahoto ministan ya na jawabi ta bakin Adeluyi, komawa ICT gadan-gadan zai bunkasa karfin tattalin arzikin kasar fiye da abin da aka gani a bana.

Jimillar tattalin arzikin Najeriya ya motsa ne da 9.5% ne a sakamakon gudumuwar da aka samu daga bangaren mai. An kuma samu gudumuwar 90.5% daga sauran bangarorin na dabam.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel