Mafi yawan wadanda za mu ba aiki ba wadanda su ka je makaranta ba ne - Keyamo

Mafi yawan wadanda za mu ba aiki ba wadanda su ka je makaranta ba ne - Keyamo

Gwamnatin tarayya ta sanar da cewa za ta dauki mutane 774, 000 aiki na musamman a fadin kasar nan. Gwamnati za ta yi wannan ne domin rage radadin annobar cutar Coronavirus.

Karamin ministan kwadago da aikin yi, Festus Keyamo, ya fito ya bayyana yadda za a bi wajen daukar ma’aikatan. Ana sa ran za a zabi mutum 1, 000 ne daga kowace karamar hukuma.

Festus Keyamo SAN ya ce mafi yawan mutanen da za a dauka wannan aiki wadanda ba su yi karatu a jami’a ba ne. Wasu su na tunanin cewa an warewa masu digiri ne wannan dama.

“Ya kamata mu sani wannan shiri na SPW, an yi shi ne akasari ga marasa kwarewar aikin hannu, da masu balaguro, da kuma mutanen da ke karkara, ba wadanda su ka gama karatu ba.”

Keyamo ya bayyana cewa gwamnati za ta dauki hayar wadanda su ke fita neman aikin kwadago ne duk ranar Duniya. Irin wadannan mutane ne gwamnatin Buhari za ta kawowa agaji.

“Duk da cewa akasari za a dauki hayar wadanda ba su iya wani aiki ba ne, za mu dauki tsirarrun mutanen da su kware a aikin hannu wadanda za su yi aikin kafinta, fenti da gini, dss.”

KU KARANTA: Gwamnatin Buhari ta fadi lokacin da za a dauki mutane 774, 000 aiki

A cewar Ministan, za a dauki matasan aiki ne gwargwadon irin ayyukan da ake bukata a kowace karamar hukuma, don haka ya karyata rade-radin cewa sharar kwata kurum za a rika yi.

“Watakila SPW ya zama aikin lokacin rani. Shirin zai taimakawa marasa hali daga cikinmu. Wannan tsari ya na cikin yadda Indiya da Bangladesh su ka fita daga kangin talauci.”

Ministan kwadagon na Najeriya ya ce idan an tashi karkare shirin, watakila a janye matasan a maida su harkar noma. Keyamo ya bayyana wannan ne da kansa a shafinsa na tuwita jiya.

“Kwamitocin jihohi na daukar aikin za su tuntubi masallatai, coci, tashoshin mota, makwabta, fadar sarakuna domin su samu sunayen ainihin masu zama a cikin karamar hukuma.”

Bayan an yi haka, ministan ya kare da cewa: “Za a fito da lambar wayoyinsu a fili domin a iya tuntubarsu a jihohinsu.” Ministan ya ce har masu Digiri za su iya jarrabar sa’arsu a shirin.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel