Korona: Jimillar ma su dauke da cutar a Najeriya ya haura 10,000

Korona: Jimillar ma su dauke da cutar a Najeriya ya haura 10,000

Sabbin mutane 307 ne hukumar yaki da cututtuka ma su yaduwa a kasa (NCDC) ta sanar da cewa sun kamu da kwayar cutar korona a Najeriya a ranar Lahadi, 31 ga watan Mayu.

A cikin sanarwar da NCDC ta saba fitarwa a daren kowacce rana, ta fitar da jerin jihohin da adadin ma su dauke da kwayar cutar su ka fito kamar haka;

Lagos-188

FCT-44

Ogun-19

Kaduna-14

Oyo-12

Bayelsa-9

Gombe-5

Kano-3

Delta-3

Imo-2

Rivers-2

Niger-2

Bauchi-2

Plateau-1

Kwara-1

Ya zuwa karfe 11:26 na daren ranar Lahadi, alkaluman NCDC sun nuna cewa akwai jimillar mutane 10162 da aka tabbatar da cewa su na dauke da kwayar cutar korona a Najeriya.

An sallami mutane 3007 daga cibiyoyin killacewa daban - daban da ke fadin Najeriya bayan an tabbatar da warkewarsu sarai daga kwayar cutar korona.

Kazalika, annobar cutar korona ta hallaka 'yan Najeriya 287.

DUBA WANNAN: Hotunan ganawar shugaba Buhari da kwamitin yaki da annobar korona a kasa

Darektan cibiyar binciken cututtuka ma su yaduwa (CIDR) a jami'ar Bayero da ke Kano (BUK), Farfesa Isa Abubakar, ya ce raguwar adadin ma su kamuwa da cutar korona a jihar abin damuwa ne.

Ya ce raguwar alkaluman ma su cutar a Kano ba ya nufin cewa jama'a ba sa kamuwa da cutar a zahiri.

Farfesan ya yi gargadin cewa raguwar alkaluman ma su kamuwa da korona a Kano ba alama ce da ke nuna cewa an fara samun saukin annobar a jihar ba.

Kwararren ya bayyana hakan ne yayin da ya ke gabatar da jawabi bayan gidajen sayen da man fetur na A. A. Rano da Aliko Oli sun bawa cibiyar CIDR gudunmawar na'urar gwajin cutar korona.

Ya yi zargin cewa gwamnatin jihar Kano ba ta bayar da adadin samfurin jinin jama'ar da ya kamata a yi wa gwajin cutar korona.

Abubakar, Farfesa a bangaren ilimin cututtuka ma su yaduwa, ya nuna damuwarsa a kan rage adadin samfur din da jihar Kano ke aikawa cibiyar gwajin cutar korona.

A cewar Abubakar, raguwar adadin ma su kamuwa da na ma su dauke da kwayar cutar a jihar Kano ba alama ce ta cewa an fara samun lafawar annobar a jihar ba.

Sai dai, jagora a kwamitin yaki da annobar cutar korona a jihar Kano, Dakta Tijjani Hussaini, ya musanta cewa gwamnati ta na kwangen aika adadin samfur din da ya kamata a yi wa gwaji zuwa cibiyar gwaji ba.

Ya bayyana cewa daga ranar 24 zuwa 30 ga watan Mayu, an aika samfur 1,018 domin gudanar da gwaji amma 70 ne kawai aka samu su na dauke da kwayar cutar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel