Dan sanda ya kashe abokin aikinsa, ya raunata jama'a masu yawa

Dan sanda ya kashe abokin aikinsa, ya raunata jama'a masu yawa

Rundunar 'yan sandan jihar Legas ta ce ta kama sifetan dan sandan da ya halaka abokin aikinsa har lahira.

A wata takarda da ta fito a ranar Lahadi, Bala Elkana, jami'in hulda da jama'a na 'yan sandan jihar, ya ce Monday Gabriel ya dinga harbi wanda ya janyo mutuwar Felix Okago, dan sanda mai mukamin sajan.

Ya ce an sauya wa Gabriel wurin aiki ne daga Abuja zuwa Ikoyi ta jihar Legas don yin aiki na musamman.

Jami'in hulda da jama'a na 'yan sandan jihar ya ce lamarin ya faru wurin karfe 4:30 na safe bayan ya illata mutane masu yawa.

Ya ce an kama sifetan dan sandan a yayin da yake niyyar tserewa ta gada ta uku a birnin Legas.

Elkana ya ce an fara bincike a kan aukuwar lamarin yayin da ake duba lafiyar kwakwalwar dan sandan.

"A ranar 31 ga watan Mayun 2020 wurin karfe hudu da rabi na safe, mun samu kiran gaggawa a kan cewa Sifeta Gabriel da ke aiki na musamman daga Abuja ya dinga harbi babu kakkautawa," yace.

Ruwan harsasai: Dan sanda ya kashe abokin aikinsa, ya raunata jama'a masu yawa
Ruwan harsasai: Dan sanda ya kashe abokin aikinsa, ya raunata jama'a masu yawa. Hoto daga The Nation
Asali: Twitter

KU KARANTA: Jigawa: Yadda 'yan bindiga suka bi ɗan kasuwa har gadon jinyarsa suka sace shi

"Sajan Felix Okago wanda ke aiki na musamman tare da sifetan, ya mutu bayan raunikan da ya samu daga harbin bindiga yayin da sifetan ya tsere ba tare da samun wani rauni.

"A yunkurinsa na tserewa, ya dauka motar sintiri inda ya doshi babbar gada ta uku yayin da yake harbi. Jami'an 'yan sandan yankin Bariga da ke Akoka ne suka kama shi tare da kwace bindigar.

"Gawar mamacin na nan a ma'adanar gawawwaki da ke asibitin 'yan sanda yayin da aka kai sifetan asibiti don duba lafiyarsa.

"Kwamishinan 'yan sandan jihar ya umarci mataimakin kwamishinan 'yan sandan jihar da su karba binciken. Rundunar na mika ta'aziyyarta ga iyalan mamacin da ya mutu yayin kare kasarsa," Ya bayyana.

Ana samun yawaitar kisan jama'a da 'yan sanda ke yi a jihar Legas.

A ranar Juma'a, rundunar 'yan sandan jihar ta damke wasu jami'ai biyu a kan kisan Tina Ezekwe mai shekaru 16 a duniya.

A makon da ya gabata, rundunar ta bayyana kama Okoro Charles da tayi, Sifeta mai aiki da ofishinsu na yankin Ikotun a kan zarginsa da ake da kisan Fatai Oladipupo.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel