Bikin karamar sallah: Kyawawan hotunan jaruman Kannywood

Bikin karamar sallah: Kyawawan hotunan jaruman Kannywood

Duk da cutar korona da ta zama ruwan dare dama duniya, an yi bikin karamar sallah cike da godiya ga Allah da ya bada damar kammala azumin watan Ramadan lafiya.

A wasu jihoin arewacin Najeriya, an samu damar sallatar Idin karamar sallah yayin da wasu kuwa aka yi sallah a gida.

Hakan kuwa bai hana jama'a cin kwalliyarsu tare da zuba hotunan bikin shagalin sallar a kafafen sada zumuntar zamani ba.

Jaruman masana'antar fina-finai ba a bar su a baya ba, da yawansu sun wallafa hotunansu a kafafen sada zumuntar zamani tare da fatan ganin sallar shekaru masu zuwa cike da koshin lafiya.

Kyawawan hotunan jaruman Kannywood da iyalansu inda suke mika godiya ga Allah a kan kammala azumin watan Ramadan mai alfarma:

Bikin karamar sallah: Kyawawan hotunan jaruman Kannywood
Jaruma Rahama Sadau da mahaifiyarta. Hoto daga BBC
Asali: Instagram

Bikin karamar sallah: Kyawawan hotunan jaruman Kannywood
Yakubu Muhammad, Sani Danja da iyalansa. Hoto daga BBC
Asali: Instagram

Bikin karamar sallah: Kyawawan hotunan jaruman Kannywood
Jaruma Saratu Gidado na fatan Allah ya maimaita. Hoto daga BBC
Asali: Instagram

Bikin karamar sallah: Kyawawan hotunan jaruman Kannywood
Rabi'u Rikadawa tare da yaransa maza. Hoto daga BBC
Asali: Instagram

Bikin karamar sallah: Kyawawan hotunan jaruman Kannywood
Hadiza Gabon da Maryam Gabon na fatan Allah ya maimaita. Hoto daga BBC
Asali: Instagram

Bikin karamar sallah: Kyawawan hotunan jaruman Kannywood
Jarumi Zahradeen Sani tare da iyalansa. Hoto daga BBC
Asali: Instagram

KU KARANTA: Cashewar matan aure a gaban mazansu: Mawaki Hamisu Breaker ya yi karin haske

Bikin karamar sallah: Kyawawan hotunan jaruman Kannywood
Jaruma Fati Washa na yi wa masoya fatan alheri. Hoto daga BBC
Asali: Instagram

Bikin karamar sallah: Kyawawan hotunan jaruman Kannywood
Ali Nuhu, Lawal Ahmad da iyalansu. Hoto daga BBC
Asali: Instagram

Bikin karamar sallah: Kyawawan hotunan jaruman Kannywood
Jaruma Maryam Yahaya tare da mahaifiyarta. Hoto daga BBC
Asali: Instagram

Bikin karamar sallah: Kyawawan hotunan jaruman Kannywood
Wankan sallan jaruma Maryam Booth. Hoto daga BBC
Asali: Instagram

Bikin karamar sallah: Kyawawan hotunan jaruman Kannywood
Jarumi Aminu Shariff da iyalansa na yi wa masoya barka da sallah. Hoto daga BBC
Asali: Instagram

Bikin karamar sallah: Kyawawan hotunan jaruman Kannywood
Baballe Hayatu na yi wa jama'a barka da sallah. Hoto daga BBC
Asali: Instagram

Bikin karamar sallah: Kyawawan hotunan jaruman Kannywood
Umar Faruk Gombe, Falalu Dorayi da abokin su a filin Idi. Hoto daga BBC
Asali: Instagram

A wano labari na daban, a cikin kwanakin shagalin bikin sallah karama ne wani sabon al'amari ya ziyarci yankin arewacin Najeriya.

An ga bidiyon matan aure daban-daban suna cashewa a gaban mazansu, lamarin da ya jawo cece-kuce daga jama'ar da suka hada da malamai, 'yan mata, samari da sauransu.

A yayin da wasu sassa na jama'a ke bayyana cewa matan auren sun yi matukar birgesu, wasu na tofin Alla-wadai garesu na fallasa sirrin zamantakewa tare da nishadinsu a kafafen sada zumunta.

BBC ta samu zantawa da mawakin wakar "Jarumar Mata" a shafinsa na Instagram kai tsaye.

Duk da mawakin ya bayyana cewa ya saki wakar ne tun a karshen shekarar 2019 kuma har tayi tashe tare da lafawa, bai taba tsammanin za ta sake tashe kamar haka.

Kwatsam ya ga matan aure na tikar rawa a gaban mazansu tare da rangaji ga sautin wakarsa.

Ya ce, "Abinda yasa na yi wakar jarumar mata shine duba da yanayin mutane. Sau da yawa idan zan yi waka, ina duba halayyar mutane ne kamar su zurfafawa wajen soyayya.

"Hakazalika, na ga kwana biyu ban yi wa masoya waka ba, shiyasa nace bari in yi musu. Amma ba budurwata nayi wa ba."

Shaharren matashin mawakin ya bayyana cewa, tsaf ya zauna ya zabi kalaman da ya yi amfani da su a cikin wakar.

A misali na baitin farko 'Ashe da rai nake son ki jaruma ba da zuciya ta ba...' wannan na bayyana cewa soyayyar ta har bayan rai ce mara sauyawa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel