COVID-19: An sallami dukkan masu korona a Zamfara

COVID-19: An sallami dukkan masu korona a Zamfara

Jihar Zamfara ta sallama majinyata biyar da suka rage mata masu fama da cutar korona a ranar 29 ga watan Mayun 2020.

Kamar yadda hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa ta Najeriya (NCDC) ta bayyana, jihar ta fara samun mutane biyu dauke da cutar ne a ranar 24 ga watan Afirilun 2020. A lokacin kuwa Najeriya na da mutum 1,095 a fadin jihohi 27 wadanda ke dauke da muguwar cutar.

Bayan makonni biyu, jihar ta samu mutum 65 da ke dauke da muguwar cutar yayin da mutum uku suka mutu amma babu ko daya da ya warke.

A ranar 11 ga watan Mayu, mutum daya ya warke amma mutane biyu sun sake rasuwa.

Bayan mako daya, NCDC ta bayyana cewa masu cutar korona a jihar Zamfara sun haura zuwa 84 amma mutum 45 sun warke. Daga bisani NCDC ta bada hakuri a kan karin mutum takwas da ta yi wa jihar.

A gyaran da tayi, ta mayar da yawan masu cutar zuwa 76 kuma an sallami 63 daga asibiti.

Ba a sake samun mai dauke da kwayar cutar a jihar ba har zuwa ranar 29 ga watan Mayu.

Amma kuma, rahoton NCDC din ya bayyana cewa mutum 71 sun warke daga cutar amma an rasa rayuka biyar.

COVID-19: Zamfara ta sallami dukkan masu korona na jihar ta
COVID-19: Zamfara ta sallami dukkan masu korona na jihar ta. Hoto daga SaharaReporters
Asali: UGC

KU KARANTA: Mun gano abinda ya janyo mace–mace a Azare – Gwamnatin Bauchi

Kafin jihar ta sallami mutum biyar na karshe, ta kasance ta 17 a cikin jihohin da suka fi yawan masu cutar a kasar nan.

Zamfara ce jiha ta biyu da ke biye da Kebbi a rashin masu cutar a ranar 29 ga watan Mayun 2020. Jihar Kebbi ta sallami mutum 12 na karshe da suka warke daga muguwar cutar a ranar 28 ga watan Mayu.

A ranar 29 ga watan Mayu, mutum 9,302 ne suka harbu da cutar a fadin jihohi 35 na kasar nan tare da babban birnin tarayya.

A wani labari na daban, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce kusan dala biliyan daya ce aka sace wa Najeriya karkashin salon mulkin soji a Najeriya.

A wata takarda da aka wallafa a Newsweek, shugaban kasar ya jinjinawa kasashen da suka dawo da kudin.

Duk da Buhari bai kira sunan Sani Abacha ba kai tsaye, amma a bayyane yake cewa yana magana a kan mulkin soji na tsakanin 1993 zuwa 1998.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel