A kalla dala biliyan daya aka wawura a mulkin Abacha - Buhari

A kalla dala biliyan daya aka wawura a mulkin Abacha - Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce kusan dala biliyan daya ce aka sace wa Najeriya karkashin salon mulkin soji a Najeriya.

A wata takarda da aka wallafa a Newsweek, shugaban kasar ya jinjinawa kasashen da suka dawo da kudin.

Duk da Buhari bai kira sunan Sani Abacha ba kai tsaye, amma a bayyane yake cewa yana magana a kan mulkin soji na tsakanin 1993 zuwa 1998.

Takardar shugaban kasar ta zo ne bayan makonni uku da kasar nan ta samu dala miliyan 311 daga Amurka.

Kasar Najeriya ta karba wasu kudaden kafin nan daga kasashen Amurka da Switzerland.

Bayan Najeriya ta sake samu wadannan kudi daga Amurka da Bailiwick, Abubakar Malami, Antoni Janar din tarayya ya ce za a yi amfani da kudin ne wajen kammala babbar hanyar Legas zuwa Ibadan, hanyar Abuja zuwa Kano da kuma babbar gada ta biyu ta Niger.

A takardar, Buhari ya ce za a yi amfani da kudin ne wajen yin kayan more rayuwa ga 'yan Najeriya.

A kalla dala biliyan daya aka wawura a mulkin Abacha - Buhari
A kalla dala biliyan daya aka wawura a mulkin Abacha - Buhari. Hoto daga Channels TV
Asali: UGC

KU KARANTA: Mutum 10 da suka fi kowa kudi a tarihin duniya (Hotuna)

"A Najeriya, an kammala matatar man fetur mai zaman kanta ta farko wacce ita ce mafi girma a duniya. Ana gab da kammala aikin Mambila wacce za ta samar da wutar lantarki ga gidaje miliyan 10," Buhari ya rubuta.

"A yanzu kuwa, za mu iya ci gaba da samar da titunan mota, titunan jiragen kasa da wuraren samar da wutar lantarki. Duk daga cikin kusan dala biliyan daya da aka sata a ka mika wa kasashen Amurka, Ingila da Switzerland," ya ce.

Ya ce Najeriya na fatan duniya ta amfana da ita, ba wai tayi ta neman taimako ba.

Shugaban kasar ya bayyana cewa Afrika na da wata babbar rawa da za ta taka na kawo gyara yayin da annobar COVID-19 ta wuce.

"Wasu za su iya cewa ya yi wuri a fara wannan tunanin. Amma ba hakan bane, akwai bukatar a fara tunani mai zurfi tun da wuri," yace.

Shugaban kasar ya ce duk da cewa babu wata kasa ko nahiya da ke da yancin kasuwa, amma Afrika na amfani da dukkan damar da ta samu wacce za ta amfani duniya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel