Mun gano abinda ya janyo mace–mace a Azare – Gwamnatin Bauchi

Mun gano abinda ya janyo mace–mace a Azare – Gwamnatin Bauchi

Hukumar Lafiya Bai Daya na jihar Bauchi ta ce binciken da ta ke gudanarwa a kan yawaitan mace–mace a jihar ya nuna cewa zubar da ciki ba bisa kaida ba da wasu ma'aikatan Lafiya wadanda basu kware ba keyi a jihar ya kashe mata 200.

Binciken na nuna cewa zubar da cikin ne dalilin mace macen da aka samu a karamar hukumar Azare da wasu kananan hukumomi a jihar ta Arewacin Najeriya kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban hukumar, Dr Rilwanu Mohammed ne ya bayyana hakan yayin taro da cibiyar wayar da kan mutane a kan harkokin Lafiya ta jihar Bauchi ta shirya.

Zubar da ciki ne ya janyo mace–mace a Azare – Gwamnatin Bauchi
Zubar da ciki ne ya janyo mace–mace a Azare. Hoto daga Naija Home Based
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Mutum 10 da suka fi kowa kudi a tarihin duniya (Hotuna)

Ya ce ba a kammala binciken ba amma sakamakon da aka fara samu ya nuna cewa zubar da ciki ne ya yi sanadin mutuwar kimamin mata inda ya kara da cewa akwai yiwuwar adadin ya dara haka.

Mohammed ya ce mace macen sun faru ne saboda juna biyu da mata masu aure da marasa aure suka samu kuma suka ziyarci ma'aikatan lafiya da basu kware ba domin cire cikin.

Ya ce rashin fahimtar muhimmancin bayar da tazarar haihuwa da rashin sanin abinda ya dace ayi a lokacin da aka samu juna biyu ya zama babban matsala a jihar.

Ya jadada bukatar da ke akwai a kan iyaye musamman mata su rika koyar da 'ya'yansu ilimin jima'i domin rage daukan juna biyu da ba a shirya masa ba inda ya ce hakan zai rage mace–mace da wasu hatsarin da ke tattare da cire ciki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel