Bango ya tsage: Yansanda sun garkame sakatariyar PDP sakamakon rikicin cikin gida

Bango ya tsage: Yansanda sun garkame sakatariyar PDP sakamakon rikicin cikin gida

Jami’an rundunar Yansandan Najeriya sun mamaye sakatariyar jam’iyyar adawa ta PDP, dake garin Lafiya ta jahar Nassarawa a ranar Juma’a, 29 ga watan Mayu.

The Nation ta ruwaito rundunar Yansandan jahar ta dauki wannan mataki ne bayan matasan jam’iyyar dake adawa da shugabancin riko na Francis Orogu sun rufe kofar shiga ofishin.

KU KARANTA: Yaya ya fille hannun kaninsa sakamakon rikici daya kaure tsakaninsu a kan budurwa

Shugaban na riko, Orogu, ya tara yan jaridu da nufin yin jawabi game da hukuncin wata babbar kotu da ta soke zaben shuwagabannin jam’iyyar na jahar ne a lokacin da matasan suka isa.

Bango ya tsage: Yansanda sun garkame sakatariyar PDP sakamakon rikicin cikin gida
Bango ya tsage: Yansanda sun garkame sakatariyar PDP sakamakon rikicin cikin gida
Asali: UGC

Isar matasan ke da wuya suka fatattaki yan jaridun da suka taru, tare da shaida musu cewa su tafi gidan Orogu su saurari jawabinsa, domin kuwa ba shi bane shugaban jam’iyyar a jahar.

Guda daga cikin yayan PDP na jahar, Adams Musa ya bayyana cewa matasan sun yi hakan ne don hana Orogu gabatar da jawabinsa game da zabukan shuwagabannin jam’iyyar da suka gudana.

Mai sharia Mustapha Ramat na babbar kotun jahar dake Akwanga ne ya soke zabukan shuwagabannin kananan hukumomi da na mazabu da aka gudanar a jahar.

Amma daga bisani Orogu ya gabatar da jawabinsa daga gida, inda ya shaida ma yan jaridu cewa zai daukaka kara domin samun adalci.

Orogu ya dage lallai shi ne shugaban riko na jam’iyyar PDP a jahar Nassarawa kamar yadda uwar jam’iyyar PDP ta kasa ta umarta, don haka hukuncin kotun ba zai kashe masa gwiwa ba.

“Muna kallon wannan hukunci da mai sharia Ramat ya yanke a matsayin wata makarkashiya da aka yi don tarwatsa kan jam’iyyarmu a jahar nan, wanda dama shi ne manufar wadanda suka kitsa rikicin.

“Saboda haka, PDP za ta kalubalanci hukuncin mai sharia Mustapha Ramat, haka zalika a siyasance ba za mu lamunci duk wani yunkuri da wasu za su yi don kawar mana da hankali ba.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel