Yaya ya fille hannun kaninsa sakamakon rikici daya kaure tsakaninsu a kan budurwa
Rikici ya balle tsakanin wasu yan biyu, watau Peter da Paul a jahar Imo a kan wata budurwa, wanda yasa Peter ya Sassari Paul da adda, daga bisani ala tilas aka datse masa hannu.
Jaridar The Nation ta ruwaito rikicin ya faru ne a ranar Litinin, 25 ga watan Mayun a kauyen Ndimoko Arondizuogu na jahar Imo, inda Peter Ogbonna ya sassare dan uwansa Paul Ogbonna.
KU KARANTA: Satar N449.5m: Hukumar EFCC ta kama babban kwamandan yan bangan jahar Benuwe
Majiyar ta bayyana cewa rikicin ya samo asali ne bayan Paul ya sa tsumagiya ya bullae dan budurwar Peter a laokacin da ya je gidansu yana neman mahaifiyarsa.
Dama Paul baya goyon bayan soyayyar Peter da wannan bazawara wanda ta haifi yara dai dai har guda biyar, amma koda Peter ya samu labarin dukan yaron da Paul ya yi sai ya harzuka.
cikin fushi Peter ya rarumi wata adda mai kaifin tsiya, ya nufi gidansu inda ya tunkari tagwayen nasa, daga nan aka fara cacar baki, wanda ya juye zuwa fada, a nan n Peter ya sassari Paul.
Jama’an dake wurin da basu tsaya wata wata ba suka garzaya da Paul cibiyar kiwon lafiya ta gwamnatin tarayya dake garin Owerri jahar, inda dole aka datse masa hannuwa don ya rayu.
Ba tare da bata lokaci ba jami’an rundunar Yansandan Najeriya reshen jahar Imo suka yi ram da mai laifin, wanda a yanzu haka yana daure a ofishin Yansanda dke Eke Ndizuogu.
A wani labarin kuma, Akalla mutane 12 wanda yawancin su mata ne aka kashe a garin Oku na karamar hukumar Boki ta jahar Cross Rivers sakamakon zarginsu da ake yi maita da tsafe tsafe.
Guardian ta ruwaito mutanen garin sun lakada ma matan dan banzan duka ne, daga bisani kuma suka cinna musu wuta wanda yayi sanadiyyar mutuwar yawanci daga cikinsu.
Sai dai wata majiya da bata bayyana kanta ba ta bayyana cwa wani babban jami’in gwamnatin jahar Cross Rivers ne ya dauki nauyin kashe mutanen.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng