Kada ku bar 'yan bindigar Zamfara su gangaro Kaduna - El-Rufai ya roki soji

Kada ku bar 'yan bindigar Zamfara su gangaro Kaduna - El-Rufai ya roki soji

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya yi kira ga dakarun sojin Najeriya da su tsananta yakar 'yan bindiga a jihar.

A cikin makonnin da suka gabata, sojin su kaddamar da manyan ayyuka a kan 'yan bindigar da suka addabi yankin arewa maso yamma ballantana a jihohin Zamfara da Sokoto.

A yayin da gwamnan ya ziyarci shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa a ranar Juma'a, El-Rufai ya nuna damuwarsa a kan yuwuwar 'yan bindigar na tserewa zuwa jiharsa.

Ya ce wannan ta'addancin babban kalubale ne ga noma da kiwo a fadin kasar nan.

"A cikin kwanaki kalilan da suka gabata ne Sokoto ta hau kanun labarai. Amma Zamfara, Kaduna, Neja da Katsina duk sun zama annoba. Muna fama da su tare da kokarin sojin Najeriya.

"Muna matukar godiya ga dakarun sojin saman Najeriya, na kasa da kuma na ruwa a kan yadda suke shawo kan matsalolin yankin kudancin Kaduna," yace.

Kada ku bar 'yan bindigar Zamfara su gangaro Kaduna - El-Rufai ya roki soji
Kada ku bar 'yan bindigar Zamfara su gangaro Kaduna - El-Rufai ya roki soji. Hoto daga The Cable
Asali: UGC

KU KARANTA: Matar aure ta zazzabga wa miji mari bayan ta kama shi budurwa a wurin cin abinci (Bidiyo)

Ya kara da cewa, "Muna fama da wannan amma a halin yanzu hankalinmu ya koma kan Sokoto da Zamfara. 'Yan bindigar da yawa za su dawo Kaduna.

"A saboda haka ne zan nemi ganawa da ministan tsaro da kuma shugabannin tsaro don karfafa ayyukan dakarun.

"Zan iya cewa sun yi matukar kokari don sun tallafa mana amma harkar 'yan bindiga babban abu ce.

"Zai shafi noma da kiwo sosai idan ba a yi komai a kai ba. Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa ya tabbatar min da cewa duk abinda ya kamata za a yi don kawo karshen 'yan bindigar."

Gwamnan ya ce abin takaici ne ganin yadda 'yan ta'addan Boko Haram suka hana arewa maso gabas sakat, su kuma 'yan bindiga suke hana arewa maso yamma.

A wani labari na daban, rayuka 15 ne suka salwanta a kananan hukumomin Faskari da Sabuwa a wani mummunan harin da 'yan bindiga suka kai yankin ranar Alhamis.

'Yan bindigar sun kai harin Unguwar Gizo, Maigora, Mai ruwa da Sabon Layin Galadima da ke karamar hukumar Faskari ta jihar.

Sun hari kauyen Machika da ke karamar hukumar Sabuwa ta jihar Katsina.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel