Katsina: 'Yan bindiga sun halaka rayuka 15, sun yi awon gaba da Shanu masu yawa
Rayuka 15 ne suka salwanta a kananan hukumomin Faskari da Sabuwa a wani mummunan harin da 'yan bindiga suka kai yankin ranar Alhamis.
'Yan bindigar sun kai harin Unguwar Gizo, Maigora, Mai ruwa da Sabon Layin Galadima da ke karamar hukumar Faskari ta jihar.
Sun hari kauyen Machika da ke karamar hukumar Sabuwa ta jihar Katsina.
Ganau ba jiyau ba, sun ce 'yan bindigar sun kai harin ne a tsakar daren Alhamis inda suka dinga barna har zuwa safiyar Juma'a.
An gano cewa, mazauna yankin sun yi yunkurin mayar da martani amma hakan sai ya jawo rashin rayuka. Mutum 15 suka rasa rayukansu inda 'yan bindigar suka yi awon gaba da Shanu masu tarin yawa.
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah, yayin tsokaci a kan yawan wadanda suka rasa rayukan su, ya ce mutum goma sha uku ne.
Ya ce, "Eh gaskiya ne, mutum 13 ne suka rasa rayukan su.
"Muna yawan jan kunnensu da su kiyaye shigewa gaba-gaba idan an kai musu hari saboda 'yan bindigar na zuwa da AK 47 ne. Ba za a iya tunkararsu da bindigar toka ba ko adda.
"Sun je satar Shanu ne kuma sai kauyawan suka tunkaresu. Hakan yasa suka halaka su."

Asali: Depositphotos
KU KARANTA: Gagaruman nasarori 3 da Buhari ya samu cikin shekaru 5 - Fadar shugaban kasa
Jaridar Punch ta ruwaito cewa akwai jami'an tsaron hadin guiwa da suka sauka a jihar don shawo kan matsalolin garkuwa da mutane da kuma 'yan bindiga.
A wani labari na daban, gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya sanar da dage dokar takaita zirga-zirga ta wucin-gadi a kowacce ranar Juma'a.
Masari ya dage dokar hana tarukan addinai da kuma yawo tsakanin kananan hukumomin jihar.
Gwamnan jihar Katsina ya ce, wannan hukuncin ya biyo bayan kokarinsu na ganin cewa Musulmi da Kiristan jihar sun yi al'amuransu na addini a kowacce ranar Juma'a tare da samo abubuwan bukata a kasuwanni.
Ya ce dole ne a samar da sinadarin tsaftace hannu a kowanne wurin bauta don amfanin masu bautar kafin shigarsu farfajiyar.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng