Babu wani abu mai muhimmanci da Buhari ya tsinana cikin shekaru 5 - PDP

Babu wani abu mai muhimmanci da Buhari ya tsinana cikin shekaru 5 - PDP

Babbar jami'iyar adawa a Najeriya PDP, ta ce babu wani abu mai muhimmanci da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tsinana cikin tsawon shekaru biyar da ya shafe a kan gado na mulki.

Shugaba Buhari wanda ya lashe babban zaben kasa a shekarar 2015, an sake rantsar da shi a wani sabon wa'adi na biyu a ranar 29 ga watan Mayu, 2019.

A wani sako da jam'iyyar PDP ta wallafa a ranar Juma'a kan shafinta na Twitter, ta ce babu abun zo a gani da Buhari zai nuna wa 'yan Najeriya a matsayin bajintar da yayi tun hawansa kujerar mulki.

Jam'iyyar ta yi zargin cewa, babu abin da ya mamaye wannan gwamnati ta Buhari illa iyaka, miyagun ababe na rashin ci gaba da durkusar da kasar nan.

Cikin sakon da ta rubuta a shafinta, jam'iyyar PDP ta ce shugaba Buhari bai tsinana komai ba face; tsananin rashawa, nauyin bashi, talauci, yunwa, rashin tsaro, kulle da hana zirga-zirga.

Shugaba Muhammadu Buhari da shugaban jam'iyyar PDP na kasa; Prince Uche Secondus
Shugaba Muhammadu Buhari da shugaban jam'iyyar PDP na kasa; Prince Uche Secondus
Asali: Depositphotos

Sauran ababen da jam'iyyar ta wassafa wadanda ta ce sun wakana a gwamnatin Buhari tsawon shekaru biyar sun hadar da; nuna wariya, danne hakki, mulkin kama karya da makamantansu.

Ta alakanta jam'iyyar APC mai ci a Najeriya da zamba, inda ta ce babu abin da ta sa a gaba face damfara gami da yaudara.

KARANTA KUMA: Adadin mutanen da cutar korona ta harba a duniya ya zarta miliyan 5 - WHO

Sai dai fadar shugaban ta ba sanarwar cewa, gwamnatin shugaba Buhari ta yi kyakkyawan tasiri a kowane bangare na kasar a tsawon shekaru biyar da ta shafe a karagar mulki.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, shi ne ya zayyana kwazon da gwamnatin shugaban Buhari a tsawon shekaru biyar din da ta yi ta na rike da akalar jagorancin kasar.

Adesina ya jaddada cewa, sauran kiris gwamnatin Buhari ta kawo karshen ta'addanci da miyagun laifuka a kasar nan.

Sai dai ya ce har yanzu akwai burace-buracen da ta sanya a gaba domin yi wa 'yan Najeriya hidima, kuma gwamnatin za ta ci gaba da zage dantsenta wajen yin aiki tukuru.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel