Kotu ta yanke wa fasto hukuncin kisa ta hanyar rataya

Kotu ta yanke wa fasto hukuncin kisa ta hanyar rataya

An yankewa wani fasto dan asalin jihar Ogun hukuncin kisa ta hanyar rataya. An kama Fasto Kolawole Samson ne da laifin kisan wani mutum mai suna Ayo Olaniyi da ke yankin Okeigbo.

Marigayi Olaniyi ya je kamo kwadi ne tare da wasu mutum uku a watan Maris 2016 a tafkin da ya kasance mallakin Fasto Kolawole.

Wata babbar kotu da ke zama a Akure ce ta yanke wa Faston hukuncin kisa. Shari’ar ta samu jagorancin Jastis Ademola Bola.

An zargi Kolawole da laifin ji wa mamacin ciwo ta hanyar amfani da adda. Daga baya ya rasu a wani asibiti sakamakon raunikan da ya ji.

Lauyoyin da suka gurfanar da mai laifi, Olusegun Akeredolu da Omotola Ologun, sun ce laifukan sun ci karo da sashi na 316 kuma abin hukuntawa ne karkashin sashi na 319 na dokokin Criminal Code na jihar Ondo.

Kotu ta yanke wa fasto hukuncin kisa ta hanyar rataya
Kotu ta yanke wa fasto hukuncin kisa ta hanyar rataya Hoto: Independent Newspaper
Asali: UGC

Mahaifiyar mamacin na daya daga cikin shaidun da aka kira a yayin da ake shari’ar.

Amma kuma Fasto Kolawole ya musanta aikata laifukan da ake zarginsa da su.

KU KARANTA KUMA: Katsina: Shahararrun 'yan bindiga 6 sun shiga hannun jami'an tsaro, an kashe wasu 2

Mai shari’a Bola ta yanke hukuncin cewa dukkan shaidun da aka mika gabanta sun gamsar da ita cewa Fasto Kolawole ne ya kashe Olaniyi.

An yanke wa Samson Kolawole hukuncin kisa ta hanyar rataya.

A wani labari na daban, bayan rufe Masallatai na sama da watanni biyu, ma'aikatar al'amuran addinin Musulunci ta yi kira ga ma'aikatanta da su fara gyara da tsaftace manya da kananan Masallatai sama da 90,000 a masarautar.

Za a bude Masallatan ne a ranar Lahadi mai zuwa amma banda Masallatan garin Makkah a wannan budewar.

Kamar yadda rahoton Saudi Gazette ya bayyana, za a bude Masallatan ne kamar yadda umarnin Ministan al'amuran addinin Musulunci, Dr. Abdullatif Al-Sheikh da kuma shawarwarin majalisar manyan malamai ta bayyana.

Ma'aikatar na yakin wayar da kai a kafafen yada labarai, Talabijin, rediyo, jaridu da sauran kafafen yada labarai.

Ana wannan wayar da kan ne don kiyaye hanyoyin yaduwar cutar ko bayan budewar Masallatai.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel