Gwamnati za ta bude filayen jirgin saman Kano, Legas, Abuja da Fatakwal

Gwamnati za ta bude filayen jirgin saman Kano, Legas, Abuja da Fatakwal

Shirye shirye sun yi nisa don bude manyan filayen tashi da saukan jiragen sama a Najeriya guda hudu bayan daukan tsawon lokaci suna garkame sakamakon annobar Coronavirus.

The Nation ta ruwaito filayen jirgin saman sun hada da Malam Aminu Kano dake Kano, Murtala Muhammad dake Legas, Nnamdi Azikwe dake Abuja da na Fatakwal jahar Ribas.

KU KARANTA: Korona: Mun fara gudanar da bincike a kan masu satar kudaden tallafi da aka bayar – ICPC

A ranar 16 ga watan Maris ne gwamnati ta hana yan Najeriya zuwa kasashe 13 da suka hada da China, Amurka da Italy, kasashen da mutane fiye dubu 100 suka mutu a sanadiyyar Korona.

Gwamnati za ta bude filayen jirgin saman Kano, Legas, Abuja da Fatakwal
Filin jirgin Abuja
Asali: Depositphotos

Gwamnati ta rufe filayen jirgin sama a ranar 13 ga watan Maris na tsawon wata daya, ta tsawaita kullewar da makonni 2, daga nan ta tsawaita shi da makonni 4 zuwa 7 ga watan Yuni.

Shugaban hukumar dake kula da sashin sufurin jirgin sama na Najeriya, NCAA, Kyaftin Musa Nuhu yace dalilin bude filayen shi ne don gudun kawo cunkoso a tsarin sufurin jirgin sama.

“Sai da muka tattauna da wakilan kamfanonin jiragen sama da sauran masu ruwa da tsaki muka yanke shawara, daga nan muka mika rahotonmu ga ministan, za mu fara aiki da filayen jirgi 4 ko 5, kuma muna fatan karawa idan har komai ya tafi yadda ya kamata.

“Ba mu son yin gaggawa don kada a samu matsala, kudi na da muhimmanci a wurinmu, amma ba zamu iya cimma tazarar mita biyu tsakanin jama’a ba, amma muna sa ran warware wannan batu nan bada jimawa ba.

“A yanzu dai mun mika ma minista shawarwarinmu, muna kuma jiran amsan da zai bamu.” Inji shi.

A hannu guda, shugaban kamfanin Air Peace, Onyeama Allen ya nemi gwamnati ta agaza ma kamfanonin Najeriya dake harkar sufurin jirgin sama domin su samu daman rike ma’aikatansu.

A wani labari kuma, Sanata Smart Adeyemi ya bayyana cewa yana matukar tausayin shugaban kasa Muhammadu Buhari saboda karyewar farashin man fetir.

Smart ya bayyana haka ne yayin da yan majalisa suke tafka muhawara game da sabon kasafin kudin 2020 da Buhari ya mika musu a ranar Alhamis, 28 ga watan Mayu.

A cewar Adeyemi, lokacin da man fetir ke da tsada a kasuwan duniya, gwamnatin lokacin ta gaza wajen karkatar da akalar tattalin arzikin Najeriya, illa satar kudaden da jami’anta ta yi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel