COVID-19: Saudi za ta bude a kalla Masallatai 90 a ranar Lahadi, ta bada sharudda 6

COVID-19: Saudi za ta bude a kalla Masallatai 90 a ranar Lahadi, ta bada sharudda 6

Bayan rufe Masallatai na sama da watanni biyu, ma'aikatar al'amuran addinin Musulunci ta yi kira ga ma'aikatanta da su fara gyara da tsaftace manya da kananan Masallatai sama da 90,000 a masarautar.

Za a bude Masallatan ne a ranar Lahadi mai zuwa amma banda Masallatan garin Makkah a wannan budewar.

Kamar yadda rahoton Saudi Gazette ya bayyana, za a bude Masallatan ne kamar yadda umarnin Ministan al'amuran addinin Musulunci, Dr. Abdullatif Al-Sheikh da kuma shawarwarin majalisar manyan malamai ta bayyana.

Ma'aikatar na yakin wayar da kai a kafafen yada labarai, Talabijin, rediyo, jaridu da sauran kafafen yada labarai.

Ana wannan wayar da kan ne don kiyaye hanyoyin yaduwar cutar ko bayan budewar Masallatai.

Daga cikin umarnin da aka bada sune: alwala a gida, wanke hannu da kyau tare da amfani da sinadarin kashe kwayoyin cuta kafin shiga ko fita daga Masallatai.

Dattawa da masu wasu cutuka na daban ana shawartarsu da su zauna a gida don yin sallar.

Ana shawartar masallata da su karanta Qur'ani a wayoyinsu ko kuma su zo da nasu amma kada su taba na Masallaci.

Ana kara kira ga Masallatan da su dinga tahowa da dardumai daga gidajensu tare da kiyaye nisan mita biyu tsakanin juna a yayin sallar.

Saudi za ta bude a kalla Masallatai 90 a ranar Lahadi
Saudi za ta bude a kalla Masallatai 90 a ranar Lahadi. Hoto daga Daily Nigerian
Asali: Twitter

KU KARANTA: Gagaruman nasarori 3 da Buhari ya samu cikin shekaru 5 - Fadar shugaban kasa

Rakiyar yara masu kasa da shekaru 15 a duniya duk an haramta.

Dole ne a dinga saka takunkumin fuska tare da gujewa musabaha a yayin shiga ko fita masallacin duk abin yi ne.

A halin yanzu, ma'aikatar addinin Musuluncin ta shawarci masu kula da Masallatan da su tsaftacesu, samar da sinadaren tsaftace hannu da sauran abubuwan bukata.

A wani labari na daban, Shugaban kasar Najeriya, Manjo Janar Muhammadu Buhari mai ritaya, ya bukaci amincewar majalisar wakilan tarayya a kan karbo sabon bashin $5.513 biliyan.

A wata wasika da kakakin majalisar wakilan Najeriya, Femi Gbajabiamila ya karanta wa majalaisar daga shugaban kasar a ranar Alhamis, ya ce za a yi amfani da bashin ne wajen cike gibin kasafin kudin 2020, daukar nauyin manyan ayyuka da wasu jihohin kasar nan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel