Katsina: Masari ya bada umarnin bude Majami'u da Masallatai, ya kafa sharadi

Katsina: Masari ya bada umarnin bude Majami'u da Masallatai, ya kafa sharadi

- Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya bada umarnin fara zuwa Masallatai da majami'u a fadin jihar

- Gwamnan ya bayyana cewa wannan hukuncin ya biyo bayan kokarinsu na ganin cewa Musulmi da Kirista sun ci gaba da bauta

- Ya tabbatar da cewa dole ne wuraren bautar su samar da sinadarin tsaftace hannu a kowanne lokaci don amfanin masu bauta

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya sanar da dage dokar takaita zirga-zirga ta wucin-gadi a kowacce ranar Juma'a.

Masari ya dage dokar hana tarukan addinai da kuma yawo tsakanin kananan hukumomin jihar.

Gwamnan jihar Katsina ya ce, wannan hukuncin ya biyo bayan kokarinsu na ganin cewa Musulmi da Kiristan jihar sun yi al'amuransu na addini a kowacce ranar Juma'a tare da samo abubuwan bukata a kasuwanni.

Ya ce dole ne a samar da sinadarin tsaftace hannu a kowanne wurin bauta don amfanin masu bautar kafin shigarsu farfajiyar.

KU KARANTA: Bana cikin gwamnatin El-Rufai - Hadiza El-Rufai

Katsina: Masari ya bada umarnin bude majami'u da masallatai
Katsina: Masari ya bada umarnin bude majami'u da masallatai. Hoto daga SaharaReporters
Asali: Twitter

A wani labari na daban, babban sakataren hukumar kula da al'amuran gaggawa na jihar Bauchi, SEMA, Shehu Ningi, a ranar Alhamis ya ce kusan mutum 15 suka rasu sakamakon nitsewar da kwale-kwale tayi a kauyen Gwaskaram da ke karamar hukumar Bauchi ta jihar.

Ningi ya tabbatar da aukuwar lamarin ne a wata tattaunawa da yayi da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Bauchi.

Ya ce kwale-kwalen na dauke da fasinjoji daga kauyen Gwaskaram inda suka nufi kauyen Yola Doka don cin kasuwa.

Ningi ya ce lamarin ya faru ne a cikin kwanakin karshen mako a rafin Gwaskaram da ke karamar hukumar Bauchi ta jihar.

Ya ce an tabbatar da mutuwar mutum 15 yayin da aka ceto mutum uku duk da dai har yanzu ana ci gaba da neman sauran.

Babban sakataren SEMA ya tabbatar cewa ana ci gaba da neman sauran gawawwakin a cikin rafin, jaridar Daily Nigerian ta tabbatar.

Ningi ya ce kwale-kwalen ta nitse ne sakamakon cika jama'a da aka yi da kuma rashin gyara. Wani rami ne gareta inda ruwa ya dinga shiga har ta nitse.

Ya ce kwale-kwalen na dauke da mutane 21 ne kuma ko daga gani an san ta yi musu kadan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel