Gagaruman nasarori 3 da Buhari ya samu cikin shekaru 5 - Fadar shugaban kasa

Gagaruman nasarori 3 da Buhari ya samu cikin shekaru 5 - Fadar shugaban kasa

Fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari ta ce a shekaru biyar da suka gabata, ta taba rayuwar 'yan Najeriya a fanni daban-daban.

An rantsar da Buhari a karo na biyu a ranar 29 ga watan Mayun 2020. A yau Juma'a ne yake cika shekaru biyar cif a kan karagar mulkin kasar nan.

Femi Adesina, mai magana da yawun shugaban kasa, ya saki wasu jawabai a kan nasarorin da shugaban kasar ya samu a cikin shekaru biyar, duk da kuwa yace tagomashin damokaradiyyar bai riga ya iso duka ba.

"Tsakanin ranar 29 ga watan Mayun 2015, lokacin da aka rantsar da shugaba Buhari a karon farko, gwamnatinsa ta yi matukar kokari wajen taba rayuwar 'yan Najeriya," yace a takardar.

"Gwamnatin ta shiga ofishin ne da niyyar kawo canji kuma an samu canjin a kowanne fanni na kasar nan. Duk da har yanzu romon damokaradiyyar yana tafe, za mu iya cewa babu dadewa zai iso.

"Bangarori ukun da gwamnatin tarayyar ta mayar da hankali sune: tsaro, farfado da tattalin arziki da kuma yaki da rashawa duk sun samu ci gaba.

"A lokacin da Buhari ya hau mulki, rashin tsaro ya yi katutu a kasar nan. Babu wanda ya taba tunanin Najeriya za ta kara wata daya ba tare da ta tarwatse ba. Bama-bamai sun zama ruwan dare da sauran laifuka.

KU KARANTA: Hedkwatar tsaro ta aike sakon gaggawa ga jihohin Arewa na tsakiya da Arewa maso yamma

"A cikin shekaru biyar, yaki da ta'addancin ya zo karshe don ana gab da kammalawa."

Adesina ya ce tattalin arziki da ya dogara da man fetur a halin yanzu an fadada shi.

Kamar yadda yace, noma da kiwo yanzu ya maye gurbin ma'adanai da ake hakowa a kasar nan.

Ya ce kasar nan na gab da samun tsaro ta fannin abinci sakamakon ire-iren abincin da ake nomawa a kasar nan.

A fannin yaki da rashawa, hadimin shugaban kasar ya ce Shugaba Buhari ya dauka dabi'ar "Aikata laifi, a hukuntaka. Babu gudu, ba ja da baya.

"Komai a bayyane yake kuma ba sai mun fadi ba," Adesina yace.

A takaice dai, ko ta yadda shugaban kasar ya tunkari annobar Coronavirus abun a jinjina masa ne.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel