Duk da Corona: Gwamnatin Benuwe za ta gudanar da zaben kananan hukumomi ranar Asabar
Gwamnatin jahar Benuwe ta sanar da shirinta na gudanar da zaben kananan hukumomin jahar a ranar Asabar duk kuwa da hauhawar adadin masu kamuwar da cutar Coronavirus a kasar.
The Nation ta ruwaito kwamishinan kiwon lafiya kuma sakataren kwamitin yaki da COVID-19 a jahar, Sunday Ongbagbo yace mutane 6 kacal suka kamu a jahar, kuma tuni hudu sun warke.
KU KARANTA: Kowa da ranarsa: Tubabbun yan bindiga sun kwato mutane 12 daga hannun yan bindigan Zamfara
Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta na jahar, Loko Tersoo ne ya bayyana haka, inda yace hukumar za ta gudanar da zaben kananan hukumomi a ranar Asabar, 30 watan Mayu.
Hukumar zaben ta sanar da haka ne ta bakin kakaakinta, Ngodoo Toryem cikin wata sanarwa da ya fitar yana cewa:
“Shugaban hukumar ya ce hukumar ta samar da tanade taanden kariya don tabbatar da lafiyar masu zabe da jami’an zabe.
“Daga ciki akwai samar da sabulun wanke hannuwa a dukkanin rumfunan zabe, rage yawan jama’a masu kada kuri’a a kowanne rumfa ta hanyar tabbatar an kada kuri’a bayan an tantance masu kada kuri’a.
“Haka zalika za’a dabbaka dokar bayar da tazara a rumfunan zabe, kuma babu wanda zai kada kuri’a ba tare da yana sanye da takunkumin rufe fuska ba.” Inji shi.
Daga karshe sanarwar ta jaddada manufar hukumar na gudanar da zaben gaskiya da gaskiya tare da tabbatar da an yi adalci a wajen gudanar da zaben.
Don haka ta yi kira ga masu ruwa da tsaki su tabbata sun bi dokokin da hukumar ta shimfida don a yi zaben lafiya a gama lafiya.
A wani labarin kuma, Sanata Smart Adeyemi na mazabar Kogi ta yamma ya bayyana cewa yana tausayin shugaban kasa Muhammadu Buhari saboda karyewar farashin man fetir.
Smart ya bayyana haka ne yayin da yan majalisa suke tafka muhawara game da sabon kasafin kudin 2020 da Buhari ya mika musu a ranar Alhamis, 28 ga watan Mayu.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng